✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi jana’izar dan majalisar Kadunan da ’yan bindiga suka kashe

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar, har da Gwamna El-Rufa’i.

Dubban jama’a ne suka halaci jana’izar dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rilwanu Aminu Gadagau da ’yan bindiga suka kashe a ranar Talata.

Daga cikin wadanda suka halarta har da Gwamnan Jihar, Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, tare da yan Majalisar Dokoki na Jihar.

A daren Litinin ne da misalin karfe 8:30 ne na ranar ’yan bindigar suka datse hanyar a daidai Dumbin Rauga, inda suka dauki tsawon lokaci suna kashe mutane.

Daga nan ne suka kwashe mutanan da ba a san yawansu ba cikin su har da marigayin.