✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi mace ta farko a matsayin ciyaman a Borno

Hajiya Inna, ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar karamar hukuma a tarihin Jihar Borno.

Hajiya Inna Galadima ta jam’iyyar APC, ta zama Shugabar Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito cewa Hajiya Inna, ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar karamar hukuma a tarihin Jihar Borno.

Hajiya Inna, ta taba rike mukamin kwamishina da kuma mukamin mai bai wa gwamnan Borno, shawara ta musamman.

Kafin Hajiya Inna Galadami, shugabar karamar hukuma mace ta farko a Jihar Borno ita ce Fanta Baba Shehu, wadda da farko aka zabe ta mataimakiyar shugabar karamar hukuma a tsohuwar jam’iar UNCP, amma daga bisani ta zama shugabar karamar hukuma ta hau kujerar sakamakon rasuwar ciyaman din.

A ranar Lahadi ne, Shugaban Hukumar Zabe na Jihar Borno, Farfesa Mohammed Konto, ya ayyana Hajiya a matsayin wadda ta lashe zaben Karamar Hukumar Jere a jihar.

Konto, ya ce ta samu kuri’u 110,459, inda ta doke abokin hamayyarta na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 2,478.

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar, ta lashe zaben kananan hukumomin jihar 27 da na kansiloli 312 da ke jihar baki daya.