✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zullumi kan yoyon bututun man fetur a unguwannin Legas

Ana tsoron tashin gobara bayan tsiyayar man a magudanan ruwan unguwanni.

An wayi gari cikin fargaba a yankin Igando/Ikotun da ke Jihar Legas inda man fetur ke ta tsiyaya da yawan gaske daga bututan mai a safiyar Juma’a.

Lamarin ya faro ne daga Layin Omoboriowo, da ke Pipeline Bus Stop, a unguwar inda aka ga man fetur na ta yoyo daga bututan da ke unguwar.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ta tabbtar da faruwar lamarin, ta kuma tura ma’aikata domin dakile yiwuwar tashin wuta daga wuraren da man ke ta tsiyaya.

Darakta-Janar na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce man fetur din na fitowa ne daga bututun mai da aka fasa.

Ya ce “Da isarmu, binciken da muka gudanar ya tabbatar cewa man fetur din na fitowa ne daga bututun man kamfanin NNPC da wasu bata-gari suka fasa da sanyin safiyar Juma’a 27 ga Agusta, 2021.

“Man fetur din na yoyo sosai a magudanan ruwa da suka karade yankunan Omoboriowo Street da Old Garage Ikotun Junction da New Garage Ikotun Junction da Kasuwar Ikotun Market da kuma Igando/Ikotun.”

A halin da ake ciki, jami’an LASEMA da ’yan sanda da kuma jami’an kashe gobara na ta kokarin shawo kan lamarin.

Ya ce, “An riga an girke motoci uku na kashe gobara, sannan ma’aikatan NNPC na kokarin toshe wuraren da man ke yoyo kafin su fara gyara bututun,” inji shugaban nan LASEMA.

Sai dai ya ce, “A halin yanzu babu labarin asarar rai ko ta dukiya, amma ana ci gaba da wayar da kan mazauna yankin domin dakile yiwuwar tashin wuta ko gobara, da ke iya haddasa asara, duba da cewa yanzu wurin yana cikin babban hadarin tashin wuta.”

Ana ci gaba da aikin shawo kan lamarin a yankunan.