✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC za ta kaddamar da manhajar neman tallafin kudi daga ’yan Najeriya

A cewar Kwamitin, manhajar za ta taimaka wajen takaita mu’amala da jakunkunan kudi a harkokin zaben 2023.  

A ranar Talata ake sa ran Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, zai kaddamar  da manhajar da ya kirkiro don neman tallafin kudi daga  hannun ’yan Najeriya.

Kwamitin ya ce ya kirkiro manhajar ‘Crowdfund’  ne don tara kudaden da zai yi amfani da su wajen tallata dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima.

Sanarwar da kwamtin ya fitar ta ce manhajar za ta bai wa ’yan Najeriya damar mika gudunmawarsu don mara wa Tinubu/Shettima baya.

A cewar Kwamitin, manhajar za ta taimaka wajen takaita mu’amala da tsabar kudi a harkokin zaben 2023.

Wannan shi ne kwatankwacin abin da ya faru yayin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a wa’adinsa na farko, inda aka kirkiro da katin waya da ya bai wa talakawan kasa damar mika gudunmawarsu ga neman zabensa.