✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta yi wa Crystal Palace raga-raga a Emirates

Nasarar ta kawo karshen koma bayan da Arsenal ta samu a wasannin da ta yi guda 3 a watan Disamba.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi wa takwararta Crystal Palace raga-raga a wasan Firimiyar Ingila da suka fafata a wannar Asabar din. 

Arsenal wadda ta kare martabar filin wasanta na Emirates, ta nuna wa Crystal Palace babu sani babu sabo duk da makwabtaka da ke tsakaninsu ta kasancewa ’yan birnin Landan.

Arsenal wadda ake yi wa lakabi da Gunners, sannu a hankali ta kwarara wa Crystal Palace kwallaye biyar rigis ba tare da kungiyar da Roy Hodgson ke jagoranta ta farke ko da kwallo daya ba.

‘Dan wasan baya Gabriel Magalhaes ya fara jefa wa Arsenal kwallo na farko a minti 11, kafin Dean Henderson ya ci gida a minti 37, abin da ya bai wa Arsenal kwallon ta na 2.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Leandro Trossard ya jefa kwallo ta 3 a minti 59, sannan Gabriel Martinelli da ya shiga canji ya jefa kwallaye biyu a mintina 94 da 95.

Wannan nasarar ta kawo karshen koma bayan da kungiyar Arsenal ta samu a wasannin da ta yi guda 3 a watan Disamba.

Haka kuma, wannan nasarar dai ta bai wa Arsenal damar komawa matsayi na 3 a teburin Firimiya da maki 43 kamar yadda Manchester City ke da shi, sai dai  City tafi Arsenal jefa yawan kwallaye, abinda ya ba ta damar zama ta biyu.