✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wainar da aka toya a manyan wasannin mako na 7 a Firimiyar Ingila

An ci Manchester ta birni da ta kauye.

A halin yanzu dai Manchester City ce ke jan ragamar teburin Firimiyar Ingila da maki 18 bayan wasanni bakwai.

Wolverhampton ce dai ta kawo karshen wasa shida a jere da Manchester City ta ci a Firimiyar a bana.

City ta yi rashin nasarar ce da ci 2-1 a hannun Wolverhapton a wasan mako na bakwai ranar Asabar a Molineux.

Wolves ce ta fara cin kwallo ta hannun Ruben Dias, minti 13 da fara tamaula, bayan da dan wasan City ta ci gida.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta farke ta hannun Julian Alvarez, amma Wolves ta kara na biyu ta hannun Hee-Chan Hwang.

Da wannan sakamakon, Wolves ta kawo karshen rashin nasara a wasa hudu a dukkan fafatawa, wadda aka doke karo uku da canjaras daya.

Tottenham da Liverpool 

Ita kuwa Tottenham doke Liverpool ta yi da ci 2-1 a wasan mako na bakwai a gasar Firimiyar Ingila da suka kara ranar Asabar.

A minti na 36 Tottenham ta ci kwallo ta hannun Heung-min Son, karo na hudu kenan da yake cin Liverpool a karawa da su.

Daga baye ne Liverpool ta farke ta hannun Cody Gakpo daf da za su je hutun rabin lokaci.

Tun kan a ci Liverpool aka bai wa dan wasanta, Curtis Jones, jan kati a minti na 26 da take leda.

Karo na uku ke nan da ake bai wa dan kwallon Liverpool jan kati a wasa bayan wanda aka yiwa Mac Allister a karawa da Bournemouth da Virgil van Dijk a wasan Tottenham.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka kara bai wa Liverpool jan kati na biyu a fafatawar, inda aka kori Diogo Jota.

Daf da za a tashi wasa ne Liverpool ta ci gida ta hannun Joel Matip, da hakan ya bai wa Tottenham maki ukun da take bukata.

Karon farko da aka ci Liverpool bayan wasa 17 a jere ba tare da rashin nasara ba tun daga Afirilun bara da cin wasa 12 da canjaras biyar.

Crystal Palace da Manchester United 

Manchester United ta sake cin karo da rashin nasara a haduwarta da Crystal Place ranar Asabar.

Palace ta doke United da kwallo 1 mai ban haushi duk da yadda aka yi tunanin farfadowar tawagar ta Erik ten Hag.

Shan kayen na Manchester United na zuwa ne kwanaki 4 bayan ta doke Crystal Palace a wasannin cin kofin Carabao.

Haka kuma, rashin nasarar da United ta yi ita ce karo na 4 cikin wasanni 7 da tawagar ta doka daga faro wannan kaka zuwa yanzu.

Da farko dai an yi tsammanin United ta dore da nasara lura da bajintar da ta nuna a wasannin Carabao amma sai Palace ta dauki fansar waccan rashin nasara.

An dai tashi wasan ba tare da tawagar ta ten Hag ta iya zura kwallo ba duk kuwa da matsa kaimin da suka yi a zagaye na biyu wato bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Erik ten Hag ya faro wasan da zaratan ‘yan wasansa na gaba 3 da suka kunshi Bruno Fernandes da Rasmus Hojlund da kuma Mason Mount a zagaye na biyu, amma duk da haka aka gaza samun sauyi.

Suka dai ta fara tsananta ga ten Hag ganin yadda ya fara kakar wasan ta bana cike da rashin nasara musamman a wasannin Firimiya ko da ya ke sun yi nasarar doke Wolves da Nottingham Forest amma kuma suka sha duka hannun Brighton da kuma yanzu a hannun Crystal Palace.

Bournemouth da Arsenal 

Arsenal wadda ake yi wa laƙabi da Gunners, ba sani ba sabo ta nuna wa Bournemouth wadda ta karbi baƙuncinta ranar Asabar a filin wasan na Vitality.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci Arsenal ta zuba wa mai masaukin baƙin kwallo biyu ta hannun Bukayo Saka a minti na 17 yayin da kuma Martin Odegaard ya sakada tashi a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 44.

Bayan an dawo hutun rabin lokacin ne kuma ta sake tisa wa kan bajintar da ta yi, inda Kai Havertz ya jefa kwallo a bugun fenariti yayin da Ben White ya rufe taro kwallonsa a mintin ƙarshe.