✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asali da tashen Murja Kunya

Auren Murja da wannan ɗan sanda bai yi ƙarko ba, inda ba a jima ba, suka rabu, daga nan ne kuma ta sake komawa kauyensu.

Murja Kunya ta kasance shahararriyar ’yar TikTok, wadda ta yi fice a shafukan sada zumunta saboda dalilai daban-daban, musamman a wajen matasa ta zama wata fitacciyar mai barkwanci ko mai samar da nishadi a shafinta.

Ga Hukumar Hisbah da kuma wasu daidaikun mutane, Murja na gaba-gaba wajen bata tarbiyyar al’umma, duba da irin abubuwan da take yadawa a shafinta na TikTok.

Za a iya cewa ga ’yan siyasa kuma Murja wata kadara ce da za ta iya taka rawa a lokutan yakin neman zaɓe.

Abu guda ɗaya da kusan kowa ya yarda da shi, shi ne, lamba ɗaya ce wajen iya ɗaukar hankalin masu bibiyarta a shafukan sada zumunta, musamman irin bidiyoyin da take wallafawa.

Wace ce Murja Kunya?

An haifi Murja Ibrahim Kunya ne a kauyen Kunya da ke Karamar Hukumar Minjibir ta Jihar Kano.

Murja ta tashi ne tare da iyayenta, wato Malam Ibrahim Kunya da kuma mahaifiyarta, Hindatu duk a kauyensu na Kunya, inda ta girma, ta yi wayo a can.

Duk da cewa babu tabbaci a kan hakikanin shekarunta, amma dai abin da ya shahara shi ne, Murja ba za ta wuce shekara 27 zuwa 28 da haihuwa ba.

An kuma tabbatar da cewa, a lokacin da take tasowa, ba ta yi wata makarantar boko ba sai dai ta yi Makarantar Islamiyya ta Fodiyya a garin na Kunya.

Haka kuma, an kara tabbatar da cewa, ba ta kammala wannan makaranta ba ta bari, sakamakon auren da aka yi mata a lokacin.

A lokacin ta auri wani ɗan sanda ne, inda kuma suka zauna a garin Minjibir wato hedikwatar Karamar Hukumar Minjibir.

Auren Murja da wannan ɗan sanda bai yi karko ba, inda ba a jima ba, suka rabu, daga nan ne kuma ta sake komawa kauyensu na Kunya, ta ci gaba da zama, sannan daga bisani ta sake wani auren a ƙauyen nasu kamar yadda wani makusancinta ya shaida wa Aminiya.

Wasu makusanta biyu sun tabbatar da cewa, bayan auren nata na biyu ta zauna ne a garin Gunduwawa, inda shi ma dai kamar wancan, bai yi karko ba.

Daga nan ne ta yi ƙaura daga ƙauyen Kunya zuwa cikin garin Kano, wajen wasu ’yan uwanta da ke Unguwar Hotoro da ke Karamar Hukumar Nasarawa.

Akwai rade-radin cewa, Murja na da ɗa guda ɗaya, amma duk lokacin da aka yi yunƙurin jin ta bakinta a kan wannan batu, ba ta cewa komai.

Murja dai kamar yadda binciken Aminiya ta tabbatar, iyayenta ba wasu masu kuɗi ba ne, don haka a lokacin da ta taso ta fuskanci matsalolin rayuwa iri-iri, saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki ita da iyayenta.

Kamar kowa, Murja ta fara amfani da shafukan sada zumunta a karon farko domin sha’awa kawai, ana haka kuma ta fara shahara, ta fara samun ’yan canji daga harkar.

Sannu a hankali ta bunkasa har ya kasance ta kafu a TikTok, inda ta yi kaurin suna da wani shafinta mai suna Yagayagamen.

Murja dai ta yi ta yunƙurin shiga Masana’antar Kannywood, amma ba ta samu karbuwa ba, wannan ya sa ta mayar da hankali a kan TikTok, inda ta ƙara shahara sakamakon irin bidiyoyin da take yadawa a kafar.

Ta ci gaba da cin karenta babu babbaka a dandalin, inda ta yi matukar shahara, musamman a tsakanin alummar Hausawa.

Kai har ta kai Murja na cikin matan da suke da yawan mabiya a dandalin TikTok, inda take da mabiya sama da mutum miliyan 1.8 a shafinta, wanda ba kowa ne ke samun wadannan magoya baya ba.

Ana cikin haka ne kuma aka fara samun sabani tsakanin matashiyar da Hukumar Hisba ta Jihar Kano, a karkashin jagorancin Malam Aminu Ibrahim Daurawa, inda har ta kai ga hukumar ta gayyace ta sakamakon wasu korafe-korafen da hukumar ta karɓa daga wasu mazauna yankin da take, inda ta ja mata kunne, sannan ta sallame ta a wancan lokaci.

Wannan dai ya faru ne a Nuwamban 2023. A wannan lokaci, Malam Daurawa, ya yi mata nasihohi daban-daban, inda ya nusar da ita irin matsalar da take tattare da yada irin bidiyoyin da ba su kamata ba a shafukan sada zumunta, wadanda ka iya janyo lalacewar tarbiyya ga yara, musamman kanana.

A lokacin ta ce ta ji wannan wa’azin kuma za ta daina sanya irin wadannan bidiyoyi a shafin nata, amma sai dai kash ba ta iya cika alkawarin ba.

Domin kuwa ta ci gaba da yada sharholiyarta kamar yadda ta saba, wanda hakan ma ya sa ta kara samun magoya baya.

Wannan ya sa Hukumar Hisba ta hasala, inda har ta kai ga hukumar ta tuhume ta da yada badala da karuwanci, wanda hukumar ta ce ya saba wa tsarin shari’ar Musulunci.

A ƙarshe dai hukumar ta yi nasarar kama ta, ta mika ta ga kotu, inda aka tsare ta har tsawon mako guda, wato zuwa ranar 20 ga watan Fabrairun 2024.

Ana cikin wannan hali ne kuma aka samu labarin cewa, wata kotu ta bayar da umurnin sakin Murja daga tsarewar da aka yi mata a gidan gyaran hali kafin a yanke mata hukunci, wanda hakan ya janyo ce-ceku-ce a jihar.

Kwatsam ana tsaka da wannan hali kura ta dan lafa, sai aka kara samun wata hatsaniyar, inda Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya fito cikin wani taro ya bayyana rashin gamsuwarsa da wasu ayyukan Hukumar Hisba, musamman wani samame na yakar yada badala da hukumar ke yi da ake yi wa take da ‘Operation Kau-da-Badala’.

Wannan kalami ya jawo wa Gwamnan suka daga mutane daban-daban, inda wasu ke ganin maganar ta Gwamnan na da alaƙa da tirka-tirkar da ke tsakanin Murja da Hukumar Hisba, wanda har wasu suka yi zargin cewa da sa hannun Gwamnan aka saki Murja, bayan tsare ta da kotu ta yi a gidan gyaran hali.

Dalili kuwa shi ne, an san cewa wannan matashiya ’yar gaba-gaba ce a masu goyon bayan Gwamnan da gwamnatinsa kuma ta taimaka kwarai a yayin yakin neman zabe, wanda shi Gwamna da kansa a yayin wani taro, ya bayyana cewa, suna sane da irin rawar da taka kuma za su taimaka mata.

Malam Daurawa a nasa ɓangaren, da fitar wannan kalami na Gwamna, ya fito ya nuna takaicinsa kuma take shi ya sanar da yin murabus daga matsayin Shugaban Hukumar a ranar 1 ga Maris, bisa abin da ya ce bai ji daɗin kalaman da Gwamnan ya yi ba.

Sai dai wasu manyan malamai da daidaikun masu fada-a-ji a kasa sun shiga maganar, inda daga baya ya janye murabus din, ya koma bakin aiki a ranar Talata 5 ga watan Maris.

Ko a 2022 sai da wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta bukaci Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya kamo tare da tuhumar Murja da wasu ’yan TikTok a jihar, bisa korafin da wasu malamai suka shigar na zargin u da gurbata tarbiyya.

Sauran wadanda ake zargin a lokacin sun hada da Mista 442 da Safara’u da Dan Maraya da Kawu Dan Sarki da Ado Gwanja da Ummi Shakira da kuma Samha Inuwa.

A ranar Litinin 25 ga Maris na 2024, Mai shari’a Nasiru Saminu na Babbar Kotu a Jihar Kano, ya bayar da belin Murja, tare da hana ta ci gaba da maganganu a shafukan sada zumunta har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar da ta shigar daban a wata kotun na dakatar da shari’ar da take yi tsakaninta da Hukumar Hisba a wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kwana Hudu.