✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayo Owodunni: Dan Najeriya ya zama Kansila a Canada

Buhari ya taya Mista Owodunni murnar lashe zaben.

An zabi wani dan asalin Najeriya mai suna Ayo Owodunni a matsayin bakar fata na farko da ya zama kansila a mazabar Kitchener da ke birnin London Ontario na kasar Canada.

Tuni dai har Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da gudunmawar da kungiyar ’yan Najeriya mazauna ketare ke bayarwa wajen daga martabar kasar a kasashen waje.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar, Malam Garba shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Buhari ya bayyana nasarar da Mista Owodunni ya samu a wannan zabe mai cike da tarihi a matsayin kwazon da ’yan Najeriya ke yi na daga martabar kasar a ketare.

Haka kuma Buhari ya ce wannan ya nuna karara yadda mutumin yake bullo da tsare-tsare na ci gaba, da goyon bayan ’yan Najeriya mazauna Canada a matsayinsa na mai bayar da shawara da kuma kokarinsa na hada kan ’yan kasar a Canada.

Shugaba Buhari ya umarci ’yan kasar mazauna ketare da su kasance jakadu na gari a duk inda suka samu kansu a fadin duniya, ya kuma shawarce su da kada su ji shakkun cimma muradunsu.

Kazalika, Buhari ya taya Mista Owodunni tare da matarsa Folake da kuma yaransu biyu murnar lashe zaben, wanda ya bayyana a matsayin “mai matukar muhimmanci.”