✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba don mu ba bala’in da ya tunkaro har Najeriya sai ya shafa — Sojin Nijar

Mun yi gaggawar karbe mulkin Nijar domin dakile mummunar barazanar da hatta Najeriya sai ta shafa.

Janar Abdourahmane Tchiani, shugaban mulkin sojin Nijar, ya ce juyin mulkin da suka yi ya ceci hatta Najeriya daga fadawa wani mummunan bala’i.

Shugaban Kungiyar Izala na Najeriya, Sheikh Bala Lau ne ya sanar da hakan yana mai cewa Janar Tchiani ya fadi hakan yayin ganawar da suka yi da shi jiya Asabar a Yamai, babban birnin Jamhuriyyar Nijar.

Aminiya ta ruwaito cewa, ganawar tawagar malaman Najeriya da ta gudana a birnin Yamai a matsayin tasu gudunmuwa domin warware rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi kasar.

A cewar Sheikh Bala Lau, Janar Tchiani ya shaida musu cewa, sun yi gaggawar karbe mulkin Nijar ne domin dakile mummunar barazanar da ba iya kasarsu kadai za ta shafa ba domin kuwa hatta Najeriya sai ta dandana kudarta.

Kawo yanzu babu wani tabbaci kan hakikinin barazanar da wannan sanarwa ta zayyana la’akari da cewa daga haka Sheikh Bala Lau bai yi wani karin haske a kai ba.

Sai dai Bala Lau ya bayyana cewa “tabbas wannan ziyara ta samu gagarumar nasara, domin kuwa da farko Firaministan kasar ne (Ali Mahamane Lememine Zeine) ya tarbe mu tun a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai, daga nan kuma ya yi mana jagora domin ganawa da Janar Tchiani a fadarsa.

Wannan lamari dai na zuwa ne a yayin da Rundunar Tsaron Najeriya ta yi zargin cewa wasu na neman tunzura ta domin yi wa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki, amma ba za ta ba da kai bori ya hau ba.

Kakakin Hedikwatar Tsaron Najeriya, Birgediya Tukur Gusau ne ya bayyana hakan a saƙon da ya aiko wa wakilinmu a safiyar Asabar, inda ya bayyana masu ƙulle-ƙullen a matsayin “miyagu marasa kishin ƙasa” ne.

Amma Janar Tukur Gusau bai yi ƙarin haske game da waɗanda yake zargin suna neman hure wa sojojin kunne ba.

“Wannan wani kinibibi ne da neman kawar da hankalin sojoji daga ainihin aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu,” in ji shi.

Ya jaddada ce duk irin zugan da za a yi musu, sojoji ba za su taɓa yin abin da zai kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya da aka samu da jiɓin goshi ba.

Birgediya Tukur Gusau ya kara da cewa, maimakon sauraron masu mugun nufi na neman juyin mulki, sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da aikinsu na kare ƙasa, kuma ba za su saurari masu neman hana ruwan Najeriya gudu ba.