✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta aika wa Nijar sojoji 100 da makamai

Lamarin na zuwa a daidai lokacin da Nijar ta buƙaci sojojin Amurka 1100 su fice daga ƙasar.

Ƙasar Rasha ta aika wa Jamhuriyyar Nijar sojoji 100 da makamai da na’urorin kare sararin samaniya.

Gwamnatin riƙo ta Jamhuriyyar Nijar ta sanar da isowar makaman da ta ce sun shigo ne albarkacin hulɗar ayyukan soji da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Tashar talbijan RTN mallakar gwamnati ta gwada wani jirgin da ta ayyana a matsayin wanda ke ɗauke da lodin makaman da suka iso birnin Yamai.

An ga isowar makaman tare da sojojin Rasha kimanin 100 da za su yi aikin girka waɗannan makamai su kuma bai wa takwarorinsu na ƙasar horo kan yadda za su yi amfani da su.

Jirgin dakon kaya samfarin ILYUSHIN 76 ne ya sauka filin jirgin saman Yamai a cikin daren Laraba zuwa wayewar Alhamis.

Bayanai sun ce jirgin na ɗauke da makaman kare kai daga hare-haren sama hade da wasu na’urorin kariyar sararin samaniya kamar yadda aka gani a wani rahoton da gidan talbijan mallakar gwamnatin Nijar ya watsa.

Wannan wani bangare ne na sabuwar huldar da hukumomin mulkin soja suka kulla da gwamnatin Vladimir Putin a ci gaba da laluben hanyoyin magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Labarin isowar sojojin horon Rasha hade da kayayyakin kare sararin samaniya na zuwa ne a wani lokacin da ake jiran ganin yadda za ta kaya bayan da hukumomin Nijar suka buƙaci Amurka ta kwashe sojojinta 1100 waɗanda ke girke a yankin Agadez da sunan yaƙi da ta’addanci.

Haka kuma, lamarin na zuwa ne yayin da a Yamai wata ƙungiyar kin jinin sojojin ƙasashen ƙetare ke shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Asabar da nufin matsa lamba ga dakarun Amurka su fice daga wannan kasa.

A wani matakin kaucewa tafka ta’asa, hukumomin birnin Yamai sun sanar da rufe hanyoyin da ke zuwa ofishin jakadancin Amurka daga karfe 7 na safiyar Asabar zuwa 1:30 na rana.