✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba zan ci gaba da fitowa a shirin ‘Labarina’ ba – Nafisa Abdullahi

Ta ce ta dauki matakin ne saboda ta samu lokacin kasuwancinta da kuma karatu.

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan, kuma daya daga cikin manyan jarumar fim din nan mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi ta ce za ta daina fitowa a cikin shirin.

Jarumar ta ce ta yanke shawarar daukar matakin ne saboda ta samu isasshen lokacin gudanar da harkokin kasuwancinta da kuma na karatu.

Nafisa ta tabbatar da hakan ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram da yammacin ranar Asabar, inda ta ce tana mai matukar takaicin yin hakan.

A sakon da ta wallafa, jarumar ta rubuta, “Happy New Year to you all🎊 Labarina Project ne da nake alfahari da shi ah duk inda na shiga.

“Saira Movies is also like my own company because mun Jima Muna aiki tare. I’m very sad to let you all know bazan ci gaba da Aikin Labarina ba, dalili shine rashin samun lokaci na yadda ya kamata, i have my own businesses, school, a company to run and also my own films that I’m planning to start shooting very soon.

“Bazan ce ah jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za’a ci gaba da film din Labarina ko da ni ko ba ni.

“Ina ba dubban masoya hakuri Akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira movies Zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi, Allah Kuma ya basu sa’a Wajen kammala sauran shirin,” kamar yadda ta wallafa a shafin nata na Instagram.