✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babangida na son Osinbajo ya yi takarar shugaban kasa

Babangida ya ce Najeriya na bukatar mutum na gari irin Osinbajo.

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyon bayansa ga Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya tsaya takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Janar Babangida ya bayyana haka ne yayin karbar magoya bayan mataimakin shugaban kasar a wata ziyara da suka kai masa a gidansa da ke Minna, a ranar Alhamis.

Babangida ya bayyana Osinbajo a matsayin mutumin kirki, kuma daya daga cikin jerin irin mutanen da Najeriya take bukata domin mulkar ta a 2023.

Ya kara jadadda goyon bayansa ga Osinbajo cewa yadda Najeriya take shan fama, mutane na gari ne wadanda suka fahimci bambamcin da ke tsakanin al’ummar kasar kadai ne za su iya tafiyar da ita zuwa tudun mun tsira.

Tsohon shugaban mulkin sojin,  ya ce ya amince ya karbi bakuncin tawagar ne saboda ya gamsu cewa Osinbajo na da halayen da za su sa shi ya yi wa Najeriya jagoranci na gari.

Sai dai har zuwa yanzu da aka lokacin kada gangar siyasa 2023 ke karatowa, Osinbajo bai bayyana aniyarsa ta yin takarar shugabancin kasa ba, amma tuni kungiyoyi suka shiga zawarcin tsawarsa.

Sai dai hasashen masu sharhin siyasar Najeriya na ganin jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ne zai tsaya takarar shugabancin kujerar a 2023.