✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Sallah: A fara neman wata, inji Sarkin Musulmi

Duban watan Babbar Sallar 2020, shekarar da cutar COVID-19 ta hana maniyyata da suka biya kudi zuwa aikin Hajji

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci daukacin Musulmin Nijeriya da su fara neman jinjirin watan Dhul Hajji daga yammacin Talata 21 ga watan Yuli.

A cikin watan Dhul Hajji ne ake aikin Hajji, inda alhazai ke hawan Arfa a ranar tara ga watan, sannan al’ummar Musulmi a fadin duniya su yi Babbar Sallah a ranar 10 ga wata.

“Talata 21 ga watan Yuli wanda ya zo daidai da 29 ga watan Dhul Qadah 1441 Hijiriyya shi ne ranar duban watan Dhul Hajji 1441 Hijiriyya”, inji sanar sanarwar da Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar dauke da sa hannun Sakataren Kwamitin Harkokin Addini a Fadar, Farfesa Sambo Junaidu, ta bukaci wadanda Allah Ya sa suka ga watan da su sanar da dagatai ko hakiman garuruwansu domin sanar da Sarkin Musulmin.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya taimaki al’ummar Musulmi wajen sauke nauyin da Ya dora musu.