✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu dalilin karin kudin wuta ko mai —Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana karin kudin wutar lantarki da na man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a matsayin abin da…

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana karin kudin wutar lantarki da na man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a matsayin abin da aka yi a lokacin da bai dace ba.

Tsohon gwamnan ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya janye karin nan take, yana mai cewa karin zai kara jefa mutane cikin halin ha’ula’i.

Kwankwaso wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC ya kuma ce gwamnati ba ta da hujjar yin karin a wannan lokacin.

Ya shawarci Shugaban Kasar da ya toshen hanyoyin zurarewar kudade a gwamnati a maimakon kara lafta wa talakawa haraji.

Ya ce, “Kusan kowace kasa a duniya yanzu kokari take yi ta bullo da hanyoyin tallafa wa jama’arta domin rage musu radadi.

“Amma abin takaici a irin wannan lokacin ne kasar take kokarin kara kudaden wadannan muhimman abubuwan.

“Zai yi wahala ka sami wani mutumin da ke goyon bayan lamarin,” inji shi.

Tsohon gwamnan wanda kuma kusa ne a jam’iyyar adawa ta PDP ya yi gargadin cewa karin na iya ta’azzara matsalolin yunwa, rashin tsaro da ma rashin aikin yi a kasa.

Kwankwaso wanda kuma tsohon ministan tsaro ne ya ce ba laifi ba ne gwamnati ta yi mi’ara koma baya a kan wata manufa muddin ta fuskanci cewa manufar ba ta dace ba.

“Tafiyar da gwamnati ta shafi samun kudaden shiga da kuma kashe kudaden, saboda haka abin da ya fi dacewa gwamnati ta yi shi ne toshe hanyoyin zurarewar kudi ba wai lafta wa jama’arta haraji ba.

“Ina tunanin in aka yi haka mutane za su fi farin ciki”, inji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan wanda yanzu haka yake ziyara a Jihar Edo domin karfafa gwiwar magoya bayan PDP gabanin zaben gwamnan da za a gudanar a jihar a kwanan nan, ya ce Najeriya na da arzikin da za ta dauki nauyin ‘yan kasarta ba tare da kara farashin ba.

Idan dai za a iya tunawa a ‘yan kwanakin nan ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin farashin da ta kira wanda ya zama wajibi sakamakon matsin tattalin arzikin da annobar COVID-19 ta jefa ta ciki.