✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar kudaden Aikin Hajji: EFCC ta cafke shugaban kamfanin Medview

Ana dai zarginsa ne da karkatar da wasu kudaden Aikin Hajji.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta cafke Manajan Daraktan kamfanin jiragen sama na Medview, Muneer Bankole, bisa zargin karkatar da wasu kudaden Aikin Hajji.

Shugaban kamfanin dai wanda ya isa hedkwatar hukumar da ke Abuja da misalin karfe 11:00 na safe.

Daga nan ne dai jami’an hukumar suka titsiye shi suka ci gaba da yi masa tambayoyi.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tsegunta wa wakilinmu cewa hukumar dai ta gayyace shi ne bisa zargin karkatar rabin kudaden da Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta biya shi don yin jigilar alhazai a shekarar 2019.

Kudaden, a cewar majiyar tamu, yawansu ya kai Dalar Amurka 900,000.

Ana dai zarginsa ne da karbar kudaden amma daga bisani ya ki aiwatar da kwangilar, sannan ya ki dawo da su.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kamen.