✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Badakalar N10bn: Kotu ta tura dan uwan Gwamnan Kogi kurkuku

Jami'in Gwamnatin Kogi da ake zargi sun hada baki da dan uwan gwamnan wajen karkatar da kudaden ya tsere

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsare Ali Bello, dan uwan Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a gidan yari kan zargin satar Naira biliyan 10 daga asusun gwamnatin jihar.

Kotun ta ba da umarnin tsare shi a Gidan Yarin Kuje ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da shi kan hada baki da Jami’in Kudi na gwamnatin jihar, Abdulsalami Hudu, wajen cire kudaden tare, suka kai wa wani dan canji ya canza musu domin biyan bukatun kansu.

Mai Shari’a James Kolawole Omotosho, ya ba da umarnin tsare Ali Bello da dan canjin da kuma Hudu, wanda a halin yanzu ya buya, kan laifuka 10 da EFCC ta gurfanar da su a kai.

Hakan na zuwa ne watanni kadan bayan dambarwar EFCC da Gwamnatin Jihar Kogi kan zargin karkatar da Naira biliyan 20 na tallafi da Gwamnatin Tarayya ta ba ta domin biyan bashin albashin ma’aikata.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ana zargin su ne da karkatar da kudaden ne a lokuta daban-daban a tsakanin shekarar 2021 zuwa yanzu.

Sai dai ko da aka karanta musu tuhumar da ake musu a gaban kotun, sun musanta zargin.

Daga nan ne lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya nemi kotu ta sa ranar fara gurfanar da su, a yayin da lauyansu, Abdulwahab Mohammed SAN, ya nemi a ba da belin su.

Mai Shari’a Omotosho ya amsa rokon, tare da ba da umarnin tsare su a Gidan Yarin Kuje, har sai su  cika sharuddan da ya sanya, sannan a ci gaba da shari’ar a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2023.

Sharuddan su ne kowannesu zai  biya Naira biliyan daya sannan ya kawo mutum biyu da kowanne zai ajiye Naira biliyan biyu da shaidar mallakar gida da kudinsa ya kai Naira miliyan 500.

Dole kuma masu tsayawar su kawo takardun bayanan bankinsu kuma su damka wa kotun takardun fasfo dinsu da takardar shaidar biyan haraji na shekara uku da suka gabata.