✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban nemi a ba ni sarauta ba —Ado Aleiro

A karon farko ma sai da na yi watsi da tayin.

Kasurgumin dan bindigar nan, Ado Aleiro, wanda a kwanan nan aka nada a matsayin Sarkin Fulani a Masarautar ’Yandoto ta Jihar Zamfara, ya ce ba shi ya nemi a ba shi mukamin ba.

Aleiro wanda ake zargi da ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yamma, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da DW Hausa.

Ya ce, “A gaskiya ban nemi wannan mukami ba, Masarautar ce ta gabatar min da tayin sarautar wanda a karon farko ma na ki amincewa.

“Bayan tattaunawa da shugabanninmu kan lamarin, sun ba da shawarar cewa kada in yi watsi da tayin tun da sabon sarkin ya dage sai lallai ya ga faruwar hakan a masarautarsa – wanda kuma hakan ce ta sa na karba.”

Aleiro ya kuma musanta zargin da ake masa na jagorantar kisan sama da mutane 100 a kauyen Kadisau da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Ya ce bai san wanda ya kitsa harin ba, yana mai cewa, “Don Allah ku je ku tambayi hakimin Kadisau; harin ramuwar gayya ne, ba ni da hannu a cikinsa, kawai dai ana zargina ne.”

Lokacin da aka samu labarin cewa za a ba shi mukami, da dama sun nuna rashin amincewarsu da hakan, amma an gudanar da bikin nada masa rawani sa’o’i bayan da masarautar ta sanar da dakatar da aikin.

Matakin bai wa Aleiro sarauta ya ta’allaka ne a kan rawar da ya taka a yarjejeniyar zaman lafiya ta baya-bayan nan da aka kulla tsakanin masarautu da ‘yan bindigar da ke addabar Karamar Hukumar Tsafe ta jihar.

Tuni dai Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya dakatar da Sarkin ’Yandoto, Aliyu Marafa tare ya haramta wa duk sarakunan jihar bai wa kowa mukami ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba.