✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta nada Sergi Barjuan a matsayin kocin wucin gadi

Barcelona na ci gaba da kulla yarjejeniya da Xavi Hernandez don karbar ragamarta.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta nada Sergi Barjuan, a matsayin kocin wucin gadi bayan sallamar Ronald Koeman a daren Laraba.

Sergi Barjuan, shi ne yake rike da Barcelona ‘B’, kuma yanzu zai ja ragamar kungiyar kafin mahukuntanta su cimma yarjejeniya da Xavi Hernandez.

Sabon kocin kuma shi ne zai jagorancin atisayen kungiyar a ranar Alhamis da zarar shugaban kungiyar, Joan Laporta, ya gabatar da shi a matsayin sabon kocin.

Sergi Barjuan, wanda tsohon dan wasan kungiyar ne ya buga wa Barcelona wasa har sau 386, sannan ya lashe kofi tara.

Amma Barcelona za ta mayar da Barjuan gurbinsa na Barcelona ‘B’ da zarar sun dauki Xavi Hernandez a matsayin kocinta.

Kazalika, Barcelona za ta kara da Alaves a ranar Asabar, inda ta ke sa ran saita al’amuranta bayan samun koma baya.