✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin Batanci: Lauyan Abduljabbar ya fice daga kotu a fusace

Lauyan da ke kare malamin daga zargin batanci ya bar kotun cikin hargowa

Lauyan da ke kare malamin daga zargin batanci ga Manzon Allah (SAW), ya bar kotun cikin hargowa da bacin rai.

Lauyan malamin, Barista Dalhatu Shehu Usman, ya fice daga kotun cikin fushi ne bisa zargin kotu ta ki ba shi dama ya yi suka ga masu gabatar da kara a lokacin da suke yi wa wanda malamin tambayoyi.

Hakan ta faru ne a zaman kotun da aka gudanar ranar Alhamis.

Ana dai zargin Abduljabbar Kabara ne da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.) da yunkurin tayar da hankulan jama’a.

Tun da farko Lauyan Abduljabbar ya nemi kotun ta ba su dama su yi roko a kan a sallami shari’ar gaba daya.

Sai dai kotun ta nuna rashin dacewar yin hakan a tsakiyar shari’a, inda ta ce hakan ba me yiyuwa ba ne sai dai a yi suka a kan ingancin cajin da ake yi wa wanda ake kara, dogaro da sashe na 390 na Kundin Laifuka na Jihar Kano na shekarar 2019.

Daga nan kotun ta bayar da dama ga masu gabatar da kara su ci gaba da yi wa wanda ake kara tambayoyin da suka fara tun a zaman shari’ar na baya.

Ana tsaka da yin tambayoyin ne lauyan wanda ake kara ya yi suka ga tambayoyin masu gabatar da kara, inda kotu ta nuna amincewarta ga tambayoyin.

A nan ne lauya Dalhatu Usman ya ci gaba da fadin maganganu ga kotun na rashin sauraren sukarsu inda kotun ta fara yi masa nasiha a kan abin da yake yi.

Sai dai bai dakatar da maganganu da yake yi ba cikin hargowa da fushi, a take ya hada litattafansa ya fice daga kotun.

Sai dai kotun ta ce duk da cewa abin da lauyan ya aikata rashin ladabi ne gareta, amma ta yi hakuri ba za kuma ta dauki kowane mataki a kan shi ba.

Kotun ta kuma dage shariar zuwa ranar 21 ga watan Yuli 2022.

Yayin tattaunawarsa da manema labarai, lauyan Abduljabbar Kabara, Barista Dalhatu Shehu Usman ya zargi kotun da hadin baki da gwamnati da kuma dan uwan wanda ake kara, wato Shaikh Karibullah Nasiru Kabara.

“Daga yadda kotun nan take gudanar da wannan shari’ar, mun fahimci cewa ta koma bangaren masu gabatar da kara wato Gwamnati da kuma Malam Karibullah Nasiru Kabara wanda kowa ya san Alkalin yaron Karibu ne, don haka shi ne yake ba wa  Alkalin umarni a kan abin da zai yi a kotun.

“Kai hatta tambayoyin da ake yi a kotun Karibu ne ya rubuta su. Mun san komai. Ai mun ji yadda Karibu ya yi taron manema labarai inda ya ce ba za a ba da belin wanda nake karewa ba,” inji Barista Shehu.

A cewarsa tun da sun fahimci kotun ba za ta yi musu adalci ba, za su daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

Sai dai a martanin masu gabatar da kara ta bakin Barista Umar Usman Danbaito, sun nuna cewa abin da lauyan wanda ake kara ya yi wa kotun abin takaici ne wanda kuma yake nuna rashin ladabi.

“Kotu ba kasuwa ba ce don haka akwai ka’idoji da lauya zai bi idan bai gamsu da salon yadda shari’a ke gudana ba, to akwai hanyoyin da ya kamata ya bi, amma ba lauya ya tashi’ ya kwashe litattafansa tare da ficewa daga kotu cikin hargowa ba.

“Wannan abin takaici ne ga aikin lauya gaba daya. Duk da cewa kotu ta bayyana cewa ta hakura da abin da lauyan ya aikata mata amma na tabbata Kungiyar Lauyoyin ba za ta yarda da wannan abin ba kuma za ta dauki matakin ladantarwa ga wannan lauya.”

A cewarsa, tun da wannan lauyan ya fice daga shari’ar to za su jira idan an sami wani lauyan da zai ci gaba da kare wanda ake zargin za a ci gaba da shari’ar a ranar da kotun ta sanya wato 21 ga Yulin 2022.