✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan rikicin wata 9, jiragen Emirates za su ci gaba da aiki a Najeriya

Daga ranar Litinin 5 ga watan Disamba 2021 jiragen kamfanin Emirates za su ci gaba da aiki a Najeriya.

Kamfanin jiragen sama na Emirates, mallakin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya dawo da harkokinsa a Najeriya, bayan wata tara da ya daina yin hakan.

Emirates wanda shi ne kamfanin jiragen sama mafi girma a duniya ya dakatar da harkokinsa a Najeriya ne wata tara da suka wace bayan takun saka tsakanin gwamnatin UAE da Najeriya a kan dokokin COVID-19.

Rikicin ya taso ne bayan hukumomin kasar sun wajabta yin gwajin gaggawa ga fasinjoji masu son zuwa can, baya ga shaidar rashin kamuwa da cutar da gwamnatin Najeriya ta amince da shi.

Najeriya ta yi watsi da hakan, lamarin da ya yi sanadiyyar dakatar da harkokin sufurin jirage tsakanin kasashen biyu, wanda a yanzu aka sasanta.

A ranar Alhamis, 2 ga Disamba, 2021, ranar bikin cikar UAE shekara 50, ta sanar cewa jiragen Emirates za su ci gaba da jigilar fasinjoji a Najeriya daga ranar Litinin 5 ga watan.

Daga ranar kamfanin zai rika jigilar fasinjoji a kullum rana zuwa birnin Dubai, inda ake yawan zuwa domin hutu ko harkokin kasuwanci daga fadin duniya.

Ta ce hakan zai kuma ba wa matafiya damar bi ta Dubai domin isa ga kasashe 120 a fadin duniya.