Bayan shekara 10, an dage haramcin amfani da babura a Yobe | Aminiya

Bayan shekara 10, an dage haramcin amfani da babura a Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
    Ishaq Isma’il Musa da Ibrahim Baba Saleh

Bayan shekara goma Gwamnatin Jihar Yobe ta dage haramcin amfani da babura masu kafa biyu a duk ilahirin Kananan Hukumomi 10 da ke Kudu da Arewacin Jihar.

Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ne ya sanar da hakan a Fadar Sarkin Nguru, inda ya ziyarta domin jajanta wa al’ummar yankin dangane da ibtila’in gobara da ya auku a Babban Kasuwar Nguru.

Gwamnan ya sanar cewa a yanzu mazauna jihar suna da ’yancin amfani da babura domin saukaka musu sufurin zuwa gonaki da sauran wuraren da suka bukata.

Ya jaddada cewa wannan sabon matakin na zuwa ne a sakamakon yanayi na ci gaban da aka samu a fannin tsaro a yankunan.

Ana iya tuna cewa, tun a shekarar 2012 da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Yobe ta haramta amfani da babura masu kafa biyu a yayin da rikicin Boko Haram ya tsananta.

Daga cikin Kananan Hukumomin da aka sahalewa amfani da baburan a yanzu sun hada da Bade, Nguru, Karasuwa, Yusufari, Machina, Jakusko, Fune, Fika, Nangere da kuma Potiskum.