✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara 13 Lalong ya yi zabe lafiya a Jos ta Arewa

Bayan shekara 13 ana tsoron tashin rikici, an yi zabe lafiya a Jos ta Arewa.

Rabon da gudanar da zaben kananan hukumomi a Karamar Hukumar Jos ta Arewa tun shekarar 2008, lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jona Jang.

Bayan zaben, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, ba  a sake yin wani zaben ba sai a wannan karon.

Ko a wannan karon, yawancin mutane ba su yi tsammani za a yi zaben lafiya a kare lafiya ba, duba da yanayin tsaro da ake ciki a jihar, wanda ya wasu masu hasashe ke ganin ba zai yiwu a gudanar da zabe ba a wasu kananan hukumomi a jihar.

Tun kafin zaben na ranar Asabar, Gwamnan Jihar Filata, Simon Bako Lalong, ya ja kunnen masu yunkurin tada zaune tsaya a lokacin zaben su shiga taitayinsu.

“Ina gargadin duk masu nemar tayar da hayaniya ko kuma saka jama’a cikin kunci da bakin ciki da cewa wannan gwamantin a shirye take kuma ba za ta lamunta ba,”  a cewar gwamnan.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta umarci jami’an tsaro da su kama su kuma hukunta duk wani mai kokarin tayar da hankalin jama’a a lokacin zaben kananan hukumomin.

Baya ga haka, ana ganin hadin gwiwa da aka samu da jami’an tsaro da kungiyoyin wayar da kai ya yi tasiri kwarai wajen gudanar da zaben lafiya.

A bangare guda, wasu na ganin rashin shigar babbar jam’iyyar adawa ta PDP zaben ya taimaka wajen gudanar da shi cikin lumana.

Jam’iyyar PDP dai ba ta samu damar shiga shiga zaben kananan hukumomin ba ne saboda dakatarwar da Babbar Kotun Jihar Filato ta yi mata saboda rikicin jam’iyar kan tsayar da dan takara.

A ranar 10 ga watan Oktoban 2021 ne Hukumar Zabe ta Jihar Filato ta sanar da ’yan takarar jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka yi nasara a zaben da aka yi a duk kananan hukumomi 17 na jihar.