✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bidiyon fyade: Tambuwal ya umarci a kama dan mashawarcinsa

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba da umurnin a kama dan Mai bashi shawara, Baffa Hayatu Tafida, da ake zargin ya yi wa…

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba da umurnin a kama dan Mai bashi shawara, Baffa Hayatu Tafida, da ake zargin ya yi wa wata buduruwa fyade tare da yada bidiyon fasikancin a shafukan intanet.

Ana dai zarginsa  ne da yin hakan da nufin lalata shirin auren da take kokarin yi da wani.

Mahaifiyar budurwar da aka sakaya sunanta, Safiya Umar ita ce tabbatar da umurnin da gwamnan ya bayar, ta kuma ce tuni aka kama wadanda ake zargin.

“Gwamna ya kira kwamishinan ‘yan sanda ya umurce shi da ya kama wadanda ake zargin da abokansa da suka taimaka wajen yada bidiyon a kafafen sanda zumunta,” inji ta.

Ta ce Tambuwal ya ce a binciki lamarin tare da tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Matashin, Baffa dai yana da shakara 17 a lokacin da ya yaudari budurwar zuwa wani Otel, inda ya yi mata fyade tana da shekara 16, tare da daukar bidiyon fasadin a wayarsa ta hannu.

Mahaifiyar yarinyar ta koka kwarai da yadda masu laifin suka tura wa wanda zai auri ‘yarta, wanda hakan ya sa ya fasa auren.

Shugaban hukumar Hisba na Sakkwato, Dakta Adamu Bello Kasarawa, ya tabbatar cewa gwamna ya sa an mayar da binciken hannun ‘yan sanda.