✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta cinna wa kayan agaji wuta a Dikwa

Kazamin harin zai kawo cikas ga agajin da zai wadaci mutun 100,000, inji MDD

Maharan kungiyar Boko Haram sun banka wa ofisoshi da kayan agajin kungiyoyin jin kai na kasashen duniya wuta a harin da suka kai a garin Dikwa, Jihar Borno.

Rohoton da muke samu daga garin Dikwa na cewa a ranar Talata mayakan sun cinna wa ofishin Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta Duniya (IOM) wuta da kuma wata cibiyar kula da marassa lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya, wadda mayakan suka mamaye ofishinta na ba da tallafi da ke garin, ta tabbatar da harin Boko Haram tare da mamaye wasu kayan kungiyoyin agaji na kasashen duniya.

Sanarwar da Babban Jami’in Agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon ta ce, “Ina bakin cikin samun labarin cewa an kai hare-haren a kan ofisoshin hukumomin agaji da wasu asitoci, aka kona wasu, wasu kuma aka lalata.

Kallon ya ce, “Kazamin harin zai kawo tasgaro ga agajin da zai wadaci mutun 100,000 da ke bukatar tallafi musamman a lokacin da ake fama da barazanar yaduwar cutar COVID-19.”

A yammacin ranar Litinin mayakan kungiyar suka kutsa garin na Dikwa inda rahotanni ke cewa sun kwace iko.