✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta harba roka a Maiduguri gabanin ziyarar Buhari

Ana zargin maharan na son kai hari filin jirgin saman Maiduguri gabannin zuwan Buhari.

Yayin da ake jiran saukar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a garin Maiduguri na Jihar Borno, kungiyar Boko Haram ta harba roka a unguwar Ngomari na garin.

Alamu sun nuna maharan na kokarin kai hari filin jirgin sama na Maiduguri ne, wanda ake sa ran saukar shugaba Buhari da misalin karfe 11 na safe, su kuma sun kai harin da misalin karfe 10:45 na safiyar Alhamis.

Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa mutane da dama sun rasu sakamakon harba rokan da Boko Haram ta yi.

Cikakken bayani na tafe…