✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram ta kashe sojoji 8, ta sace mutum 100 a Borno

Mayakan Boko Haram bangaren ISWAP sun kashe akalla sojoji takwas, suka raunata 3 a wani harin kwanton bauna da suka kai wa sojojin a garin…

Mayakan Boko Haram bangaren ISWAP sun kashe akalla sojoji takwas, suka raunata 3 a wani harin kwanton bauna da suka kai wa sojojin a garin Kukawa na Arewacin Jihar Borno.

Haka kuma sun sace kusan mutum 100 a kwana 10 da suka wuce, ciki har da matasa da mata a tsakanin Kukawa da makwabtanta, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa Aminiya.

A Maigumeri kuma, a ranar Litinin ce ’yan ta’addan suka kai hari a wani asibiti, inda suka kashe wata mata, suka sace magunguna da kayan asibitin sannan suka kona asibitin.

Aminiya ta samu bayanin cewa ’yan ta’addan sun fito ne neman abinci da makamai da kudi da kuma neman karin mutane da za su tursasa su mayar da su mayaka.

Wakilinmu ya yi korarin jin ta bakin Hedikwatar Tsaro kan harin, amma Shugaban Tsare-tsarenta, Manjo Janar John Eneche bai ce komai ba.

Sai dai kafin nan, ya ce sojoji sun kashe ’yan ta’adda kusan 20 a yankin.

Yadda aka kashe sojoji a Kukawa

Wata majiya ta wa Aminiya cewa an umarci sojojin ne da su tafi Kukawa a ranar Talata domin fuskantar ’yan Boko Haram da suke addabar yankin, inda suke yawan fitowa suna sace kudade da abinci da kuma kama mutane suna tafiya da su, ciki har da mata.

A kan hanyarsu ta tafiya ce mayakan Boko Haram suka musu kwanto , wanda ya nuna alamar sun samu labarin suna hanya.

A wani labarin da ba a tantance ba, an ce ’yan ta’addan sun mamaye Kukawa, amma har zuwa lokacin hada wannan labarin ba a tantance sahihancin labarin ba.

Majiyarmu ta ce, “Sojojin Runduna ta Musamman ta 401 ne aka yi wa harin kwanton baunar. ’Yan ta’addan sun sanya kayan sojoji ne da jajayen huluna, inda suka kai wa ayarin sojojin su 28.

“A nan suka kashe sojoji 8, suka raunata 3, sannan ba a ga manyan sojojin biyu ba, amma daga baya aka gano su.

“Mayakan sun kwace motar yaki mai sulke daya da motar daukan marasa lafiya da sauransu. Sannan suka kona babbar motar yaki ta APC.”

Yadda Boko Haram suka sace akalla mutum 100

Aminiya ta kuma gano cewa sama da mutum 100 Boko Haram din ta sace a garuruwan Kukawa da Magumeri da Abadam da Marte da sauran garuruwa makwabtansu domin ko dai karbar fansa, ko mayar da su ’yan ta’adda.

’Yan ta’addan sun shigo ne da misalin karfe hudu na yamma, inda suka yi awon gaba da matasa da mata.

“Wasu iyayen suna biyan fansa su karbo ’ya’yansu. Wasu matan ana aurar da su ne ga ’yan ta’addan, sannan kalilan daga cikinsu da suka yi turjiyya kuma a kashe su.

A 2 ga watan Agustan bana ne dai mutanen Kukawa suka koma garinsu bayan kwashe kimanin shekara biyu a sansanin gudun hijiya a Maiduguri.