✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci hadin kan kasashen Afirka wurin yaki da ’yan ta’adda

Ya bayyana kaduwa da kisan da ’yan ta’adda suka yi wa mutum 70 a iyakar Jamhuriyar Nijar da Mali.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa “’Yan ta’adda sun zama tamkar shaidanun da suke yada barna a tsakanin al’umma za kuma su ci gaba da ta’addancin matukar ba a hada kai an dauki mataki ba.”

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, a yayin da yake magana kan kisan da ’yan ta’adda suka yi wa mutum 70 a yankin Zaroumdareye, kan iyakar kasar Nijar da Mali.

Buhari, ya yi Allah-wadai da faruwar lamarin, ya kuma kira da a samar da hadin kai a tsakanin shugabannin kasashen Afirka kan yaki da ayyukan ta’addanci.

Ya ce: “Hakika na razana ainun da jin labarin kisan mutane masu yawa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da ’yan ta’adda suka yi wa kisan gilla.”

Ya ci gaba da cewa, “Muna fuskantar kabarburanmu a sakamakon kalubalen tsaro da rudin shaidanun ’yan ta’adda da ke yankin Sahara kuma hadin kai da juna ne kadai mafitar da zata taimaka mana wurin yaki da ayyukan ta’addanci da makiyan ci gaban mutane.

“Rashin tabbas na daga cikin kalubalen da Afirka ke fuskanta ta fuskar sha’anin tsaro da sauransu,” inji shi.

Ya yi waiwaye kan abubuwan da suka faru a kasar Libya da cewa, “Tarwatsa Libya a shekarar 2011 shi ne musabbabin tabarbarewar sha’anin tsaro a sauran kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nigar da Chadi da Kamaro da sauran kasashe.

“Satar makamai daga Libya bayan kawar da Shugaba Gaddhafi ya haifar da hadarin gaske ta yadda makamai suka shiga hannun ’yan ta’adda, lamarin da yanzu ya haifar da kalubalen ta fuskar sha’anin tsaro ga sauran kasashe.

“Kanmu a hade yake a lamura da dama, wajibi ne a kanmu mu dauki matakin yakar wadannan shaidanun da suke far wa mutanen da ba su ji  ba, ba su gani ba.

“Ina amfani da wannan damar wurin nuna damuwa da jajanta wa gwamnati da jama’ar kasar Nijar da ’yan uwa da abokan arzikin mutanen da iftila’in ya ritsa da su,” inji Shugaba Buhari.