✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da Antonio Guterres a Aso Rock

Wannan ce ziyarar shi ta farko zuwa Najeriya tun bayan darewar shi kan kujerar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a Fadar Aso Rock da ke Abuja.

Yayin ganawar dai, sun tattauna batutuwan da suka shafi yaki da ta’addanci da samar da abinci da ma sauran batutuwan da suka shafi kasa da kasa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Buhari ya karbi bakuncin Mista Guterres ne da misalin karfe 3:00 na yamma, kafin daga bisani su sa labule don ganawar sirri kan batutuwan da suka shafi Najeriya, Afirka da ma duniya baki daya.

Babban Magatakardan wanda ya zo Najeriya ziyarar aiki ta kwana biyu ranar Talata, ya ziyarci birnin Maiduguri na Jihar Borno, inda ya gana da wadanda rikicin ta’addanci ya shafa da kuma tubabbun ’yan boko Haram.

Gabanin ganawar tasa da Buhari, ya kuma jagoranci aikin dasa furanni domin tunawa da wadanda harin bam ya rutsa da su a ginin ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Najeriya a Abuja a shekarar 2011.

Wannan ce dai ziyarar Babban Magatakardan zuwa Najeriya ta farko tun bayan darewar shi kan kujerar.

Kafin isowar shi Najeriya, Guterres ya kuma ziyarci kasashen Senegal da Jamhuriyar Nijar. (NAN)