✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta je kama tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello

Wani babban jami'in EFCC ya tabbatar wa Aminiya cewa sun kai samamen ne da nufin kama tsohon gwamnan

Jami’an Hukumar Yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Bello da ke Abuja.

Wakilinmu ya is layin Benghazi a unguwar Wuse da gidan na Yahaya Bello yake, inda ya ga jami’an na EFCC.

Wani babban jami’in EFCC da ya bukaci wakilin namu ya sakaya sunansa ya tabbatar cewa sun kai samamen ne da nufin kama da Yahaya Bello.

Sai da kuma jami’in ya ki amsa tambayar wakilin namu game da zargin da hukumar ke wa tsohon gwamnan.

Ana dai tunanin samamen na da alaƙa da badaƙalar Naira biliyan 84 na jihar Kogi a zamanin mulkin Yahaya Bello da EFCC ke bincike a kai.

Kokarin wakilinmu na samun karin bayani daga kakakin EFCC, ya ci tura.