✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada sabbin Manyan Sakatarori

Nan gaba za a sanar da ranar rantsar da su da kuma ma'aikatun da za a tura su

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin Manayan Sakatarori hudu a ma’aikatun Gwamantin Tarayya.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta sanar da haka, ta wata sanarwa da Darektar Yada Labarai a ofishinta, Olawunmi Ogunmosunle, ta fitar.

Sabbin Manyan Sakatarorin su ne James Sule daga Jihar Kaduna da kuma Ismaila Abubakar daga Kebbi. Na ukun ita ce Ibiene Patricia Roberts daga Jihar Ribas sa kuma Aliyu Shinkafi Shehu daga Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar da za a rantsar da su da kuma ma’aikatun da za a tura su.