✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sauka a London domin ganin likita

Buhari ya isa London a safiyar Talata domin ganin likita na kimanin mako guda.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari isa kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa a safiyar Tatala.

Shugaban Kasar ya tafi ganin likita na kimanin mako guda ne a birnin London na kasar Birtaniya, kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta sanar.

A safiyar Talata Hadimin Shugaban Kasa kan Kafofin Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad, ya wallafa bidiyon saukar shugaban a filin jirgi, bayan isarsa London.

Tun a ranar Litinin, sanarwar da mai magana da yawun shugabna kasa, Femi Adesina, ya fitar ta ce, shugaban, “Zai dawo Najeriya  mako na biyu na watan Nuwanba da muke ciki.”

Tafiyar tasa ganin likita na zuwa ne bayan dawowarsa daga Taron Duniya kan Sarrafa Tsirrai da ya gudana kasar Koriya ta Kudu a makon jiya.

A lokacin taron na Kasar Koriya ta Kudu, Najeriya ta Kulla yarjejeniyar gyara matatar mai ta Kaduna (KRPC) da kamfanin Daewoo, wanda a halin yanzu yake aikin gyaran matatar mai ta Warri.