✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sauka a Maiduguri

Mazauna Jihar sun yi masa waken Oyoyo Baba!

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Miaduguri, babban birnin Jihar Borno a ranar Alhamis.

Jirgin shugaban ya sauka da misalin karfe 9 da rabi a Filin Jirgin Saman Kasa-da-Kasa da ke babban birnin Jihar.

Saukarsa ke da wuya mazauna Jihar suka fara yi masa lale maraba cikin annashuwa da bayyana farin ciki suna waken ‘Oyoyo Baba’.

Ya samu tarbar Gwamna Babagana Umara Zulum da wasu manyan jami’an gwamnati da hafsoshin soji.

Sanarwar da Fadar Shugaban ta fitar ta ce shugaban zai fara kai ziyara Fadar Shehun Borno, sannan ya gabatar da jawabai ga dakarun soji kan yanayin tsaron da yankin Arewa maso Gabas yake ciki.

Shugaban zai kaddamar da rukunin farko na gidaje 10,000 wadanda ya amince a gida domin sake tsugunar da yan gudun hijira.

Haka kuma zai  kaddamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar ta aiwatar da suka hada da bude sabuwar Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Njimtilo da Jam’iar Jihar Borno.

Daga nan kuma shugaban zai zarce Barikin Maimalari inda zai ziyarci dakarun da suka jikkata a filin daga.

Ana iya tuna cewa, ziyara ta karshe da Shugaba Buhari ya kai Jihar Borno ita ce ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda aka samu wani dandazo na mutane da suka yi masa ihun “ba ma yi, ba ma yi.”