✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyara kasar Portugal

Za a karrama Buhari da lamba girmama da ta fi kowacce a kasar Portugal

Shugaba Buhari zai kai ziyar aiki kasar Portugal inda za a karrama shi da lambar giramamawa da ta fi kowacce a kasar.

Fadar Shugaban Kasa ta ce Buhari zai kai ziyarar ce a ranar Talata, bayan Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa ya gayyace shi domin su tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasashen.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce a lokacin ziyarar, za a ba wa Buhari lambar girmamawa mafi girma a kasar Portugal, wato ‘Great Collar of the Order of Prince Henry.’

A lokacin ziyarar Buhari da Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa za su jagoranci taron kasashen biyu, gami da sanya hannu kan yarjejeniya kan wasu batutuwa.

Buhari zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar, inda zai gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Augusto Santo Silva da  kuma Fira Minista Antonio Costa.