✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi ya yi maganin masu siyasar kudi —Buhari

Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ya rage kwana takwas a yi zaben Shugaban Kasa da ke tafe ranar 25 ga watan Fabrairu,…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana sane cewa canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi, ya karya lagon masu siyasar kudi.

Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ya rage kwana takwas a yi zaben Shugaban Kasa da ke tafe ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Ya kara da cewa, “Ina sane da cewa sabuwar dokar kudin ta taimaka matuka wajen karya lago da tasirin siyasar kudi.

“Wannan babban sauyi daga abin da saba a baya, kuma manoniya ce game da matakin da gwamnatin nan ta dauka domin tabbatar da an yi sahihin zabe cikin adalci.”

A jawabinsa ga ’yan Najeriya kan matsin rayuwar da suka shiga kan takaddamar da ake yi kan sauyin takardun N1,000, N500 da kuma N200, Buhari ya yi yana sane da halin da suka shiga kuma hakan ya dame shi.

Ya ce yana sane da matsaolin da wasu bara-gurbin jami’an banki ke jefa al’ummar Najeriya cikin kuncin rayuwa ta hanyar taskace sabbin takardun kudin da CBN ya ba su, suna hana ’yan Najeriya.

Shi ya sa aka umarci hukumomin EFCC da takwarorinsu da hadin gwiwar CBN su dauki mataki a kansu.

Ya jaddada cewa sabbin tsare-tsaren sun dace da manufar gwamnatinsa da kuma aniyarsa ta farfado da tattalin arziki, bunkasa tsaro dak uma toshe kofofin satar kudi da safarar kudaden haram a Najeriya.

Buhari ya kara da cewa, daga cikin nasarorin da tsarin sauyin kudin, an dawo da kashi 80 na tsabar kudaden da ke yawo a hannun jama’a zuwa bankuna.