✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Canjin Naira: EFCC ta dana wa gwamnoni tarko —Bawa

Gwamnoni da suka ajiye makudan kudade a gidajensu suna neman komawa biyan albashi a kan tebur

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta fallasa yadda wasu gwamnoni da ke shirin yin almundahanar biliyoyin kudade ta hanyar biyan albashin ma’aikata ta kan tebur.

Shugabna EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya shaida wa Aminiya a wata hira ta musamman cewa, gwamnonin sun shirya yin hakan ne a matsayin daya daga cikin dabarunsu na kawar da haramtattun biliyoyin takardun Naira da ke makare a hannunsu.

“Bayanan sirri da muka samu sun gano wasu gwamnoni da suka ajiye makudan kudade a gidajensu da sauran wuare, yanzu suna kokarin su biya albashi a kan tebur,” in ji Bawa.

Ya bayyana cewa, gwamnonin da Hukumar take bibiya sun hada da wasu biyu daga yankin Arewa, na ukunsu kuma daga Kudu.

Aminiya ta tambaye shi ko EFCC za ta gayyaci gwamnonin su amsa tambayoyi, inda ya kada baki ya ce hukumar tana bibiyar lamarin sosai.

Ya ce, “Dole mu hana su kuma muna kan aiki, amma ba su riga sun biya albashi da kudaden ba tukuna.

“Amma wannan babban lamari ne,” domin ya saba Sashe na 2 na Dokar Haramta Safarar Kudade.

“Dokar a bayyane take: Duk mutumin da zai yi harkar kudi na sama Naira miliyan biyar a wata cibiyar kudi ya haramta; na kamfanoni da hukumomi kuma kada ya wuce N10m.

“Me ya sa sai yanzu kwatsam za su kirkiri biyan albashi a kan tebur, bayan a baya ta banki suke biyan ma’aikata?

“Za su bullo da dabaru iri-iri, za su yi kokarin tantance jami’ai da sauransu,” in ji shugbana na EFCC.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da kai wa cibiyoyin ’yan canji samame a yunkurinta na dakile masu rike da haramtattun kudade da ke fadi-tashin rabuwa da su ta hanyar mayar da su kudaden kasashen waje.

Canjin takardun kudade

Hakan kuwa na zuwa ne bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirinsa na soke tsoffin takardun N200, N500 da N1,000 da kuma maye gurbinsu da wasu sababbi da ta buga.

A ranar 26 ga watan Oktoba Aminiya ta kawo rahoton sanarwar CBN na sauya takardun kudaden, da kuma sakin sabbin da aka buga a ranar 15 ga watan Disamba.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce hakan na daga matakan magance wasu matsaloli da ke illa ga daranar Naira da ma tattalin arzikin Najeriya.

Ya kara da cewa hakan zai gurgunta tattalin arzikin ’yan ta’adda, da kuma yadda mutane ke boye tsabar kudade, wanda hakan ya saba doka.

Babban bankinn ya sanya 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da takardun kudaden na yanzu za su dai na aiki.

Yadda ake rububin neman Dala

Sai dai tun bayan sanarwar ta ranar, manyan ’yan sisaya da ’yan kasuwa ke neman kokarin rabuwa da haramtattun kudaden da ke hannunsu.

Hakan ya sa suke rububin da sayen kadarori da neman canza kudaden kasashen waje — matakin da ya haifar da fargaba.

Wannan yanayi ya sa Dala tashin gwauron zabo, daga Naira 744 a makon jiya zuwa N882 a ranar Alhamis a kasuwar bayan fage a Abuja.

Hakan kuwa na zuwa ne duk da samame da kamen da EFCC ta yi a cibiyoyin ’yan canji a jihohin Kano da Legas da Abuja.

Majiyoyi sun shaida Aminiya cewa masu ’yan canji sun shiga neman Dala ruwa a jallo a fadin Najeriya, saboda yadda masu ‘mahaukatan’ tsabar kudi ke neman ta ido rufe.

Hakan ya kai ga yanzu ’yan canji na kukan rashin Dala duk kuwa da karuwar masu nemanta.

Wani dan canji a unguwar Zone 4 a Abuja ya ce masu zuwa neman Dala na yin musu tayin Naira 900 a kan Dala daya, saboda yadda ta yi karanci.

Rububin sayen kadarori

Shugaban na EFCC ya kuma tabbatar mana cema masu irin wadancan kudade na rububin sayen gidade da sauran kadarori.

“Muna sane. Ko ka sayar da kadararka ka karbi kudi, kudin da ka karba zai tashi aiki ranar 31 ga Janairu, 2023, saboda haka dole sai ka kai su banki.

“To ya za ka yi? Kwasar miliyon kudaden za ka yi zuwa banki ko kuwa?Shi ya sa muke aiki tare da bankuna, su sanar da mu idan suna da irin wadanan bayanan,” in ji shi.

Za mu ci gaba da kai wa ’yan canji samame

Ya ce samamen hukumar kan ’yan canji na da muhimmanci kuma za ta ci gaba da kawa.

Samame ga “’yan canji na da muhimmanci saboda yawancin masu makudan nairori a ajiye za su so mayar da su Dala ko kudaden wasu kasashe, shi ya sa.

“Saboda saurin yardar ’yan canji, a shirye suke su karbi kudaden daga hannun masu su, su ba su kudaden kasashen waje.

“Shi ya sa ’yan canji ke da matukar amfani a wannan aiki da muka fara,”  in ji Bawa.

Da aka yi masa magana game da yadda Dala ke tashin gwauron zabo, Bawa ya ce, rububin sayen ta ido rufe da ake yi ne ya haifar da hakan.

Ya ce masu sayen ta ido rufe na yin hakan ne ba don su yi amfani da ita wajen kasuwanci ba, sai dai su ajiye ta a maimakon kudaden da ke hannunsu a matsayin kadara.

Dalilin ganawarmu da bankuna —Bawa

Ya ce tattaunawar da hukumar ta yi da wakilan bankuna a Legas ta yi shi ne da nufin tafiya tare da su, saboda duk inda aka je, aka dawo, bankuna za a kai haramtattun kudaden.

“Mun san mutane da yawa sun boye kudaden kuma za su yi kokarin yadda za su fitar da su domin maye gurbinsu da sababbi.

“Saboda haka duk yadda aka yi, ko kadara aka saya ko tsabar kudaden ne, karshenta dai banki za a kai duk kudaden.

“Shi ya sa bankuna ke da muhimmanci a wannan tafiya. Mun kuma tsara yadda za a yi, kuma mun amince — wanda ya sayar da gida dole ya sanya kudaden a banki, haka shi ma dan canji, dole ya sanya kudaden da ya canza daidai da kimar kudaden kasar da ya ce,” a cewarsa.

Babu abin damuwa

Bawa ya bai wa ’yan Najeriya tabbaci cewa babu abin damuwa a sauyin kudaden da gwamnati ke shirin yi.

A cewarsa, ba wani sabon abu ba ne, abu ne da ya kamata duk bayan shekara biyar zuwa takwas a ce CBN ya yi.

 

Daga: Hamza Idris, Isam’ail Mudasshiru da Sagir Kano Saleh