✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

CBN zai hukunta bakunan da ke karbar yagaggun kudi

CBN ya ce zai fara hukunta bankunan da ke karbar ajiyar yagaggun kudi.

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sha alwashin hukunta bankunan da suke karbar yagaggun kudade daga hannun abokan huldarsu.

CBN ya yi wannan gargadi ne a wani mataki na hana karba da kuma ajiyar kudaden da suka tsufa da yawa.

A wata sanarwa da Daraktan Sashen Gudanarwa na CBN, Ahmed Umar ya fitar a Abuja, ya ce matakin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilu.

Umar ya ce samuwar irin wadannan takardun kudi na kawo koma baya ga tattalin arziki da kuma sha’anin kasuwanci, kuma yana bude hanyar aikata damfara.

Ya ce daga za a fara cin bankuna tarar kashi 400 bisa 100 na abin da suka karba na yagaggun kudaden da suka ajiye.

“Hukumomin Babban Bankin na CBN sun lura da cewa an samu karuwar ajiyar yagaggun kudade, kuma ya bukaci a sauya wannan kudaden.

“Kasancewar kudin a cikin tattalin arzikin yana karya darajar kudin da ke yawo a tsakanin al’umma, kuma yana iya zama hanyar aikata damfara.

“Saboda haka, duk wani tsohon kudi da aka samu a asusun ajiya na bankuna, za a ci su tarar kashi 400 na adadin abin da suka adana,” a cewar sanarwar.