✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Cin kashin da ake wa ’yan Arewa a Kudu ya isa haka’

Kungiyar ta shawarci Gwamnatin Tarayya da johohi su su shawo kan matsalar tsaro.

Kungiyar ‘Northern Reform Organzation’ (NRO) mai rajin kare kimar Arewacin Najeriya, ta yi tir da irin kisan da ake yi wa ’yan Arewa mazauna Kudu.

Kungiyar ta ce ba zai yiwu a ci gaba da zuba ido haramtacciyar kungiyar IPOB tana kashe ’yan Arewa da ke zaune a Kudu babu gaira, babu dalili ba.

Sanarwa da sakataren kungiyar, Abdulkadir Yusuf Gude ya fitar ta kuma bukaci al’ummar Arewa da su ci gaba da zama da juna lafiya ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba a tsakaninsu ba.

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su yi duk mai yiwuwa don kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankunan Arewa da ma Najeriya baki daya.

Wannan ba shi ne karo na farko da wata kungiya ko mutane ke kira da a magance irin cin kashi da ake yi wa ’yan arewa mazauna Kudu ba.

Matsalar tsaro dai musamman a Arewa, na ta ta’azzara duk kuwa da irin kokarin da jami’an tsaro ke yi.