✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Ciwon Daji na kashe mutum dubu 700 duk shekara a Afirka —WHO

Akwai hasashen samun karuwar mace-macen zuwa kusan mutum miliyan daya duk shekara.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan mutum dubu 700 ke mutuwa sakamakon ciwon daji duk shekara a nahiyar Afirka.

Wannan dai a cewar WHO na faruwa ne yayin da a kowacce shekara a kan samu kusan mutum miliyan 1.1 da ke kamuwa da ciwon a nahiyar.

Daraktar Hukumar Mai Lura da Kasashen Afirka, Dokta Matshidiso Moeti, ce ta bayyana haka ranar Lahadi a wani jawabi da ta gabatar a bikin Ranar Yaki da Ciwon Daji ta Duniya mai taken ‘Inganta Hanyoyin Yaki da Cutar: Mu hada muryoyinmu domin daukar mataki’.

Ta ce hasashen da aka yi yanzu na nuna cewa akwai barazanar samun kashi 50 cikin dari na yaran da ake haihuwa da cutar a nahiyar Afirka zuwa shekarar 2050.

Ta kara da cewa, alkaluman sun nuna cewa akwai hasashen samun karuwar mace-mace sakamakon cutar kansa zuwa kusan miliyan daya a kowacce shekara zuwa 2030, idan ba a dauki matakan da suka dace ba.

Dokta Moeti ta ce kasashe 12 ne a nahiyar Afirka ke da kyakkyawan shirin yaki da cutar.

Jami’ar ta WHO ta ce Hukumar na taimaka wa kasashe 11 domin samar da ko inganta shirye-shiryensu na yaki da cutar.