✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Jihohi 14 da aka samu karin mutum 131 da suka kamu

An samu karin mutum 131 da cutar Coronavirus ta a fadin Najeriya kamar yadda alkaluman Hukumar NCDC suka tabbatar. Hukumar NCDC mai Yaki da Cututtuka…

An samu karin mutum 131 da cutar Coronavirus ta a fadin Najeriya kamar yadda alkaluman Hukumar NCDC suka tabbatar.

Hukumar NCDC mai Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasar ce ta sanar da hakan a daren ranar Litinin cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Alkaluman sun nuna an samun karin mutum 131 da cutar ta harba da suka hada Legas (64), Ribas (12), Kaduna (11), Filato (9), Jigawa (8), Bayelsa (6), Ondo (5) da Ebonyi (4).

Sauran su ne Abuja (4), Osun (14), Borno (1), Kano (1), Ogun (1), da Oyo (1).

Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 161,868 a fadin Najeriya yayin da kuma an sallami mutum 148,125 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka.

Kazalika, a jimillance alkaluman sun nuna cutar ta kasha mutum 2,030 a fadin kasar tun daga bullarta a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu.