✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta sake karuwa a Turai —WHO

A bayan nan an kawo karshen saka takunkumi da nuna takardar shaidar karbar allurar rigakafin Covid-19 a Faransa.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cutar Coronavirus ta sake karuwa a cikin wasu kasashen Turai wadanda suka yi gaggawar soke matakan rigakafi na yaki da annobar.

Darektan WHO Reshen Turai Hans Kluge ya ce Coronavirus ta sake yaduwa a karkashin nau’in BA2 a Jamus da Birtaniya da Faransa da Italiya da cikin wasu kasashen guda 18 cikin 53 da ke yankin na Turai.

A yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a Maldovia, Hans Kluge ya ce akwai kyakkyawan fata game da makomar Turai, amma matakan da gwamnatocin nahiyar suka dauka, shakka babu zai haifar da da mara ido.

Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO ta ce a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an samu sabbin mutane sama da miliyan biyar da suka kamu da cutar, yayin da wasu sama da dubu 12 suka mutu a Turai.

Ya ce babban dalilin da ya haifar da karuwar shi ne mai yiwuwa sabon nau’in BA2, wanda ke saurin yaduwa, amma kuma duk da haka be kai sauran nau’o’in hadari ba.

Dangane da bayanan WHO, adadin sabbin alkaluman cutar Coronavirus a Turai ya ragu sosai bayan wani matakin kololuwa da aka kai a karshen watan Janairu.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar tun bayan barkewar ta zuwa kusan miliyan 194.4 sannan adadin wadanda suka mutu ya zarce miliyan 1.92.

Aminiya ta ruwaito cewa an kawo karshen saka takunkumi da nuna takardar shaidar karbar allurar rigakafin Covid-19 a Faransa, matakin da gwamnatin kasar ta dauka a ranar Litinin ta makon jiya.

Wannan mataki dai ya nuna cewa ga dukkan alamu Faransawa sun yi na’am da shi na kara tabbatar da cewa ana gab da shawo kan annobar kamar yadda Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito.

Wannan matakin na nufin cewa Faransawa da ke bukatar zuwa gidajen cin abinci ko kuma gidan kallo ko kuma shakatawa, hadi da wuraren baje koli, suna da damar zuwa ba tare da wata tsangawa ba.

Haka zalika babu batun amsa tambayar rashin dalilin sanya takunkumi a makarantu, ko a katafaren kantuna, wanda hakan ke nufin jama’a za su gudanar da harkokin su ba kamar yadda aka saba ba kafin lokacin dokar kulle.

Amma gwamnati yanzu haka ta tabbatar da cewa wuraren da ake samun cunkoson jama’a, misali motocin safa, da asibitoci ya zama wajibi mutane su kare kai, tare da baiwa kamafanoni masu zaman kan su zabi, ko su ci gaba da amfani da dokar Covid-19 din ko kuma su kyale jama’a haka nan.

An samu raguwar labarin catar Covid-19 sakamakon yakin da ke wakana tsakanin kasashen Rasha da kuma Ukraine, a gefe guda kuma batun takarar shugabancin kasar Faransa, inda masana ke ganin cewa annobar da ta kawo tsaiko a bangarori da dama a duniya ta yi nisa sosai.

A zahiri, bayan makonni da samun raguwar yaduwar cutar, hukumomin lafiya a Faransa sun ce adadin sabbin cututtukan sun haura 73,000 a ranar Juma’a, kadai daga 60,000 a mako daya da ya wuce.

Abin da kwararru ke cewa har yanzu shi ne, gwamnati kuma ta gaza cim ma burinta na kawo karshen adadin marasa lafiya da ake jibgewa a sashen ba da agajin gaggawa ko kuma killacewa kasa da 1,500.