✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Gwamnatin Kano ta raba takunkumi 10m kyauta

Don yakar cutar a fadin jihar, Gwamnatin Kano ta raba kyautar takunkumi.

A ci gaba da kokarinta na hana yaduwar cutar COVID-19 a Jihar Kano, gwamnatin jihar ta raba wa jama’a kyautar takunkumi sama da guda miliyan 10.

Kwamishinan Muhalli, Dokta Kabiru Ibrahim-Getso ya ce gwamnatin ta ga dacewar raba takunkumin ne saboda yaki da cutar a jihar.

Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kano ta kuma yi feshi a kasuwanni, wuraren ibada, makarantu da sauran wuraren taruwar mutane.

Getso ya kuma ce Ma’aikatar Muhallin ta yi feshin magani a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, da sansanin daukar horon masu yi wa kasa hidima.

Ma’aikatar ta kuma dauki mutum 200 da za su ke shiga lungu da sako don fadakar da al’umma kan cutar COVID-19.

Ya ja hankalin jama’ar jihar da su ci gaba da amfani da takunkumin fuska tare da sauran matakan kariyar COVID-19.