✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai mutum 25 gidan yari saboda karya dokar COVID-19 a Kano

Kotu ta ci tarar mutum 102 da daga cikin wadanda aka kama da karya dokar COVID-19.

Kotun hukunta masu karya dokar kariyar COVID-19 a Jihar 25 ta tura mutum 25 da ta kama da laifi gidan yari.

Akalla mutum 200 ne jami’an tsaro suka tsare saboda karya dokar COVID-19 da Gwamnatin Kano ta shimfida wanda daga cikin mutanen aka ci wasu tara.

“Mun gode Allah mutanen Kano na bin dokar sanya takunkumi don kare lafiyarsu.

“Duk masu kunnen kashi da suke kin saka takunkumi za su fuskanci hukunci. Don haka dokar kariyar COVID-19 ta zauna ke nan,” a cewar Shugabna Hukumar Kula da Hanya ta Jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba DanAgundi.

Bayan fara aiki da dokar sanya takunkumi, Gwamnatin Kano ta kafa kotun tafi-da-gidanka akalla 21, wanda DanAgundi ke jagoranta.

Ya bayyan cewa an kama masu karya dokar har mutum 102 da aka ci tarar N5,000 kowanensu.

Ya sake jan hankalin shugabanin kasuwanni da tabbatar da bin dokar kariyar.

Da yake jawabi, Kwamishinan Yada Labaran jihar, Muhammad Garba ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da kare mutane daga kamuwa da cutar COVID-19.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jihar tun bayan sake bullarta a karo na biyu.

Ya ce duk wanda kotun tafi-da-gidanka ta samu ya karya dokar to za a hukunta shi yadda doka ta tanada don haka ya ja hankalin jama’ar jihar  da su kasance masu bin doka a kodayaushe.