✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Covid-19: Likitoci 20 sun mutu a Najeriya cikin mako daya

A yayin da guguwar annobar coronavirus ta sake kada wa a duk fadin duniya, akalla likitoci 20 sun mutu a fadin Najeriya cikin makon da…

A yayin da guguwar annobar coronavirus ta sake kada wa a duk fadin duniya, akalla likitoci 20 sun mutu a fadin Najeriya cikin makon da ya gabata kamar yadda Kungiyar Likitocin Najeriya NMA reshen birnin Abuja ta bayyana.

Shugaban Kungiyar NMA reshen Abuja, Dokta Enema Amodu ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin zanta wa da manema labarai a babban birnin kasar.

Ya ce: “A cikin makon da ya gabata kadai, mun rasa furofesoshi, matuntuba, da kuma manya da kananan likitoci wanda hakan ya nuna cewar har yanzu wannan kwayar cutar tana nan tare da damu.”

Ya ce “duk da irin wannan hadarin da likitoci suke fuskanta, alawus din na wata-wata dangane da rintsin da suke shiga naira dubu biyar ne kacal.”

Ya bukaci Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamilda, da ya gabatar da kudirin da za a nazari kan alawusu din rintsi da likitoci suke suke shiga duba da yadda suke wahala har ta kai ga mutuwa.

Ya ce sun a fatan Gwamnatin Najeriya za ta shiga sabuwar shekaran da kafar dama wajen gaggauta inganta musu alawus dinsu na wata-wata.

Ya kara da cewa suna kuma bukatar ingatatattun kayan aiki na zamani musaman magunguna, takunkumin rufe fuska, sunadarin tsaftace hannu da makamantansu.