✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar mahaifin Kwankwaso a Kano

Sheikh Aminu Daurawa ne ya jagoranci jana'izar da dubun dubatar mutane suka halarta

A Yammacin ranar Juma’a aka sanya gawar marigayi Musa Saleh Kwankwaso a makwancinta, bayan babban malamin nan na Ahlus Sunnah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci sallar jana’iza.

Dubban mutane sun yi tururuwa a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke kan titin Miller a Unguwar Bompai domin nuna alhininsu kan rasuwar mahaifin nasa da ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 93 a duniya.

Daga cikin mashahuran mutane da suka halarci sallar jana’izar da aka gudanar bayan sallar Juma’a, akwai tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, Sanata Rufa’i Hanga, Kawu Sumaila, Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Murtala Sule Garo da kuma takwaransa na Ma’aikatar Raya Karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso.

Sheikh Daurawa wanda ya jagoranci sallar jana’izar, ya yi addu’ar Allah Ya jikan mamacin tare da rokon Ya bai wa iyalansa juriya da kuma hakurin rashin da suka yi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a daren ranar Juma’a ne Allah Ya yi wa mahaifin Sanata Kwankwaso rasuwa bayan ya shafe tsawon shekaru 93 a doron kasa.

Mamacin kafin rasuwarsa shi ne Hakimin Madobi kuma Makaman Karaye, Dan Majalisar Sarki kuma daya cikin Masu Zaben Sarki a Masarautar Karaye.

Marigayin ya zama Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano na farko lokacin da Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada shi a shekarar 2000.

Alhaji Saleh Kwankwaso wanda ajali ya katse masa hanzari bayan wata ’yar gajeruwar rashin lafiya, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya 19 da kuma jikoki da dama.