✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta bulla a Fadar Shugaban Kasa, ta kama Garba Shehu da wasu hadiman Buhari

Ko a makon nan sai da Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi, sai ta neme su.

Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja na nuni da cewa wasu hadiman Shugaban da dama sun kamu da cutar COVID-19.

Kafar yada labarai ta Premium Times ta rawaito cewa daga cikin wadanda suka kamu akwai Dogarin Shugaban Kasa, Yusuf Adado da babban mai tsaron Shugaban, Aliyu Musa da kuma kakakinsa, Malam Garba Shehu.

Jaridar ta kuma rawaito cewa an gwada su ne tare da tabbatar da suna dauke da cutar a cikin makon nan.

Kazalika, rahoton ya kuma ce Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, na cikin wadanda suka kamun.

Sai dai Aminiya ta gano kusan dukkan wadanda suka kamun ba a cikin matsanancin hali suke ba, saboda an yi musu cikakkiyar rigakafin cutar.

Rahoton, ya ambato Garba Shehu yana cewa, “Ba ni da tabbaci a kan abin da kuka fada, amma gaskiya ne, na kamu da samfurin COVID-19 ba mai tsanani ba.

“Ina jin dama-dama saboda an min rigakafi har hawa uku, garau nake jin kaina, yanzun nan ma na kammala motsa jikin da nake yi kullum na tsawon sa’a daya,” inji Garba Shehu.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da samfurin cutar na Omicron ke ci gaba da yaduwa.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi zagaye na uku na rigakafin cutar na kamfanin Pfizer-BioNtech.

Kazalika, a cikin makon ne dai mai dakin shugaban, Hajiya Aisha Buhari ta umarci dukkan ma’aikatanta su tafi hutu har sai ta neme su.