✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Za a yi wa shugaban Rasha rigakafi a asirce

Ya shaidawa ’yan jarida cewa, “Amma wannan karon sai dai ku yi hakuri, ba a gabanku za a yi ba.

Za a yi wa Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin allurar rigakafin COVID-19 da yammacin ranar  Talata a asirce, a daidai lokacin da kasar ke kokarin wayar da kan jama’a su karbi rigakafin da aka sarrafa a kasar.

Da safiyar Talata ne dai shugaba Putin ya bayyana cewa za a yi masa rigakafin inda zai bi sahun sauran takwarorinsa na kasashen duniya daban-daban, ciki har da Shugaba Joe Biden na Amurka da Fafaroma  Francis da kuma Sarauniyar Ingila, Elizabeth.

Sai dai sabanin mafi yawancinsu da aka yi musu a bainar jama’a, Putin ya ce a asirce za a yi masa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito.

Kakakin gwamnatin kasar, Dmitry Peskov ya ce shugaban mai kimanin shekaru 68 a duniya bai taba tsoron idon jama’a ba kusan shekaru 20 din da ya kwashe a kan mulki.

Ya shaidawa ’yan jarida cewa, “Amma wannan karon sai dai ku yi hakuri, ba a gabanku za a yi ba.

“Ba ya son a yi mishi allurar a bainar jama’a, sam ba ya kaunar yin hakan.

“Duka nau’i uku na rigakafin da aka sarrafa a Rasha na da tasiri, kuma daya daga cikinsu za a yi wa shugaban,” inji Peskov, ko da yake bai fadi wanne nau’i daga ciki za a yi wa shugaban ba.

Kasar Rasha dai ta sarrafa nau’uka uku na rigakafin da suka hada da Sputnik V da EpiVacCorona da kuma CoviVac.

Sai dai gangamin wayar da kan jama’a a kan su karbi rigakafin na tafiyar hawainiya in an kwatanta da wasu kasashen, sai dai kakakin gwamnatin kasar ya ce mutanen kasar ba sa bukatar sai an yi wa shugaban a bainar jama’a kafin su yarda suma a yi musu.