✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da gangan aka lalata layin samar da lantarki a Najeriya —Ministan Lantarki

An yi nasarar magance matsalar ta hanyar amfani da wani layin samar da lantarkin da ke Calabar.

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu katsewar lantarki ne a wasu sassan kasar sakamakon yadda aka lalata layin samar da lantarkin na Odukpani Ikot Ekpene.

Sanarwar da Ministan Lantarki Aliyu Abubakar ya fitar ranar Lahadi ta ce an samu katsewar lantarkin kusan 400MW, wanda ya haifar da rashin wuta a sassan Najeriya.

An fuskanci katsewar lantarki a sassan Najeriya tun ranar Juma’a musamman a manyan biranen da ke Kudu da Arewacin Kasar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Lantarki Isa Sanusi ta ce an yi nasarar magance matsalar ta hanyar amfani da wani layin samar da lantarkin da ke Calabar.