✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Da sana’ar tuyar kosai na gina gidaje —Inna Mai Kosai

Dattijuwar ta ce ta fi shekara 40 tana sana'ar tuyar kosai.

Wata dattijuwa da ta shekara 40 tana sana’ar tuyar kosai, ta ce sana’ar ta yi mata komai, domin da sana’ar ta gina gidaje biyu kuma take taimakon ’yan uwa da abokan arziki.

Malama Amina Ibrahim, wadda aka fi sani da Inna Mai Kosai ya yankin Dutsen Kare-kare da ke Unguwar Rogo a garin Jos, ta shaida mana cewa har yanzu ita tashi da talatainin dare ta surfa wakenta ta kai markade sannan ta tuya kosan ta sayar.

A hirarta da wakilinmu a kofar gidanta inda take sana’ar tata, Inna Mai Kosai, wadda ke sayar da kosai sau biyu a kullum — safe da yamma — ta shaida mishi cewa tun tana budurwa take sana’ar, ta kuma sana’ar ta yi mata asin-da-asin.

Malama Amina ta ce har yanzu da kwarinta kuma ta gwammace ta yi aikinta da kanta, duk da cewa za ta so ta samu ma’aikata da za su taimaka mata.

Ta ce tun kafin ta yi aure ta fara sana’ar tuyar kosai a garinsu, Michika, Jihar Adamawa.

Bayan ta yi aure kuma sai ta lura cewa zama ba nata ba ne, babban abin da ke gabanta shi ne dole ita ma ta fara neman na kanta.

Hakan ne ya sa bayan ita da mijinta sun dawo garin Jos da zama, ba ta bata lokaci ba ta ci gaba da sana’ar, wadda a dalilinta ta mallaki gidaje biyu, take kuma daukar dawainiyar sauran abubuwa.

Sai dai ta ce fafutukar cimma hakan na da matukar wahala domin takan tashi da tsakar dare a kullum don fara shirye-shiryen gudanar da harkokin yau da kullum.

Wasu masu sayen kosai da Malama Amina a wurin da take sana’ar tata a Unguwar Rogo, Jos, Jihar Filato. (Hoto: Ado Abubakar Musa).

Ga abin da ta bayyana wa Aminiya  hirar tasu:

“Nakan tashi da misalin karfe 3.30 na asuba in fara shiri; kafin nan kuma sai na jika waken, saboda idan na tashi zan surfa a turmi sannan in kai inji a markada min.

“Ni da kaina nake yin aikina, ba na bayarwa a yi min, domin idan ka ba wa wani za ka samu bacin rai, saboda na sha jarabawa, amma bukata ba ta biya.

“Zan so a ce na dauki ma’akata da za su rika taimaka min, amma hakan bai yiwu ba, saboda abin da na shaida maka; Tabbas akwai gajiya, amma gara na daure na yi da kaina.

“Zuwa karfe 7 na safe na gama shirin fara tuya kosai saboda na san zuwa karfe 7.30 na safe masu saye sun fara layi.

“Kullum a kan lokaci nake fitowa saboda ba na so mutane su zo su samu ni ban fito fito ba, saboda yawancinsu da kosan nawa suke yin karin kumallo.

“Da haka ne na samu na rike kwastomomina na tsawon shekaru, shi ya sa za ka manya da kanana, maza da mata suna zuwa sayen kosai a wurina,” inji Amina Mai Kosai.

Abin da nake da kudaden da na samu

Da take bayyana yadda ta gina gidaje da kudaden da ta samu daga sana’ar tata, dattijuwar ta ce ba a dare daya ta gina gidajen ba.

“Ba a lokaci guda na gina gidajenba, saboda ni ba mai kudi ba ce; abin da na yi shi ne, na shiga adashin  wata-wata, wanda duk wanda ke ciki ake bukatar ya yi zubi a kullum.

“Duk kudin da ka zuba, a karshen wata za a ba ka kwasa, saboda haka duk kudin da na kwasa a karshen wata tarawa nake yi, da suka kai taru sosai sai na sayi fili, na fara ginawa a hankali, har na kammala.

“Da muka tare a gidan da na fara ginawa sai na ci gaba da adashin, bayan wasu shekaru na kara tara kudaden, na sayi fili da su na gina a hankali, sai na sa ‘yan haya a ciki.

“Gidan da nake ciki ma na ba da hayar wasu dakuna, saboda dakunan da ke gidan sun yi min yawa,” a cewar dattijuywar.

Amina ta ci gaba da bayyana cewa sana’ar ta taimaka wa iyalinta ta yadda ko da mijinta ba ya nan ko kuma ba shi da kudi sai ta ciyar da gidan kafin ya dawo ko ya samu kudin ya biya ta.

Ya ce, “Yanzu mijina ya rasu, amma har yanzu ina iya kula da iyali.

“Na yi imanin cewa abin da nake yi daga ribar da ake samu a sana’ar, nufin Allah ne kawai, domin yana magance matsaloli da dama. Sana’ar ta taimaka mini sosai,” inji ta.

Shin akwai magaji?

Da aka tambaye ta ko ta horar da ’ya’yanta ko jikokinta don yin sana’ar, sai ta ce “A’a, ban horar da kowa daga cikinsu ba saboda mahaifinsu bai so hakan ba, duk da cewa ya bar ni na yi sana’ar.

“Duk lokacin da ya dawo gida, yakan tambaye su inda suke don tabbatar da cewa ban tura su talla ba.

“Ya kasance mai kulawa sosai ta yadda ba zan iya gagancin dora musu talla ba, ko sayar da kosai. Don haka, don mu zuna laiyfa da kyautata dangantakata da shi, na yi mishi biyayya.

“Lokacin da suka girma, na aurar da su; Yanzu, babu ko mutum daya daga cikinsu a gaba na, sai jikokina wadanda su kuma ba na son su yi sana’a saboda duk maza ne.

“Sanaa’ar kosai ko talla ba ta dace da ’ya’ya maza ba, sana’a ce ta mata.

“Ina da jikoki bakwai da nake kula da cinsu da tufatar da su saboda iyayensu talakawa ne kuma ba su da karfin daukar irin wannan nauyin. Har ma na aurar daya daga cikin jikokin nawa,” inji Inna Mai Kosai.

Ina so in je aikin Hajji

Malama Amina ta ce, bayan wadannan nasarori da da ta samu daga sana’ar, tana son ta kara samun kudin da za ta biya aikin Hajji.

Ta ce, “Hajji daya ce daga cikin rukunan Musulunci kuma ina fatan in sauke farali kafin in koma ga Allah.

“Ba abu ne mai sauki mutum ya tara wannan makudan kudade ba, musamman a yanzu da abubuwa suka yi tsada, amma ina fata nan gaba kadan in samu in yi aikin Hajji. Ba abun da ya gagari Allah.”

Wasu kwastomomi suna jira a zuba musu kosai a wuin Inna Mai Kosai. (Hoto: Ado Abubakar Musa, Jos).

Kwastomomin Inna Mai Kosai

Daya daga cikin kwastomomin Amina da ke Anguwar Rogo, Muhammadu Tasi’u, ya ce ya shekara sama da 15 yana sayen kosai a wurinta, inda ya ce ko da ta sauya wuri sai ya bi ta zuwa sabon wurin.

Ya ce, “Na saba da kosanta a tsawon shekaru, domin a lokacin da nake makarantar firamare iyayenmu sukan aiko mu mu saya a wurinta.

“A wancan lokacin, idan muka sayi kosan Naira 80 zai ishi kowa a gidan, amma yau na Naira 150 ba zai ishe ni ni kadai ba saboda yadda yanzu abubuwa suka yi tsada sosai.

“Ina jin dadin kosanta sosai, shi ya sa nake ci gaba da saye a wurinta.”

Shi kuma Jamilu Abdullahi, wani mazaunin yankin, ya ce ya shafe sama da shekara 20 yana sayen kosai a wurin dattijuwar.

“Na fi shekara 20 ina sayen kosanta mai dadi, domin ba ta hada shi da gari ko wani abu don samun karin riba.

“Shi ya sa nake bin ta duk inda ta je, ga shi kuma kosan nata dandanonsa daban ne, ”in ji shi.

Dattijuwa Amina ta ce ba za ta iya tuna wani babban kalubalen da ta taba fuskanta a sana’ar tata ba.

“Ban taba fuskantar wani babban kalubalen kasuwanci ba a yayin da wannan sana’ar tawa ke bunkasa. Maimakon haka, cigaba nake samu.

“Don haka, ba zan iya tuna wani kalubale a wannan harkar ba. Yawancin lokaci ina da jari mai karfi don ci gaba da ita.

“Na tuna cewa lokacin da na fara sana’ar, kwanon wake nake saye, amma yanzu na koma sayen buhuna.