Da yiwuwar PSG za ta dauki Ronaldo daga Juventus | Aminiya

Da yiwuwar PSG za ta dauki Ronaldo daga Juventus

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo
    Abubakar Muhammad Usman

Makomar dan wasan gaba na Juventus, Cristiano Ronaldo na ci gaba da daukar hankali, sai dai dan wasan a yanzu ya fi mayar da hankalinsa a gasar Euro 2020 da kasarsa ta Portugal ke bugawa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar dan wasan ya fara tattaunawa da kungiyar Paris Saint-Germain don komawa can.

  1. 2023: Zan nemi shawarar tsayawa takarar shugaban kasa — Kauran Bauchi
  2. Jami’an tsaro na aiki tare da ’yan bindiga —Gumi

Jaridar Corriere dello Sport, ta ruwaito cewa wakilin dan wasan, Jorge Mendes zai tafi birnin Paris nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, don tattaunawa da wakilan PSG kan komarwa Ronaldo kungiyar.

Budurwar dan wasan Georgina Rodriguez, a kwanakin baya ta bayyana cewar Ronaldo zai ci gaba da murza leda a Juventus.

Makomar Ronaldo

A yanzu haka babu wata jarjejeniya da wata kungiya ta cimma da dan wasan ko wakilinsa, sai dai wasu alkaluma na nuna cewa ko da zai bar Juventus, akwai yiwuwar ya koma Real Madrid, duk da kungiyar taki bata nuna sha’awa a kan dawowarsa ba.

PSG da Manchester United sun nuna sha’awarsu tun a baya na son daukar dan wasan, ko kuma su yi musayar ‘yan wasa wajen daukarsa.

A kwanakin baya an hangi wakilin dan wasan Jorge Mendes a birnin Paris, wanda ana tsammanin ziyarar tasa zuwa birnin na da alaka wajen ganin PSG ta dauki Ronaldo ne.

Kazalika, alamu sun nuna dan wasan ba shi da sha’awar ci gaba da zama a Juventus biyo bayan rashin kwazon da ta yi a kakar wasannin da aka kammala.