Daga Laraba: Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a | Aminiya

Daga Laraba: Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a

Masu bautar kasa yayin kidaya kuri’a
Masu bautar kasa yayin kidaya kuri’a
    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao da Bilkisu Ahmed

Domin sauke shirin latsa nan

So da dama bayan an kammala jefa kuri’a, masu zabe kan dakata su ga abin da zai ture wa buzu nadi – suna kasawa su tsare, a kirga, a kuma sanar da sakamako.

Hakan na faruwa ne saboda wasu matsaloli da kan kunno kai bayan an gama kada kuri’u, wani lokaci har a yi ta kai ruwa rana. Don haka masu zabe ke son su san ko ’yan takarar da suka zaba sun kai bantensu.

Shirin Daga Laraba na yau za ku ji irin abubuwan da ke biyo bayan jefa kuri’a, kama daga kidaya kuri’u, har ma da dalilan da zabe ke kasancewa inkonkulusib.